Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a jihar Jigawa sun cafke wani matashi dan shekara 22 kan zargin satar babur na abokin mahaifinsa.
Kakakin hukumar NSCDC a jihar, CSC Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da cafke shi a Birnin Dutse ranar Asabar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba.
- NSCDC Ta Kama Barayin Kebur Da Suka Yi Shigar Injiniyoyi A Abuja
- NSCDC Ta Lalata Haramtattun Matatun Mai 10, Ta Kafa ‘Yan Sintiri
Shehu ya ce, wanda ake zargin mazaunin kauyen Madara ne da ke karamar hukumar Azare ta jihar Bauchi, an kama shi ne a kauyen Sundumina da ke yankin Birnin Kudu a jihar Jigawa bisa zargin satar babur da kuma keta dokar da ta saba wa dokar Penal Code ta jihar.
“An kama wanda ake zargin ne da misalin karfe 1:00 na rana, biyo bayan samun wani rahoton daukar babur din da ya sace domin sayarwa a kasuwar maki-mako ta kauyen.
“Bayan kama shi, sai ya amsa cewa ya shiga gidan makwabcinsa, wani mai suna, Malam Muhammad l, kuma abokin mahaifinsa, ya sace babur dinsa (Boxer) ya kai Sundumina da niyyar sayar da shi,” in ji Shehu.
Kakakin ya kara da cewa wanda ake zargin ya saci baburin tun ranar 13 ga Satumba, ya ajiye shi kuma ya jira har washegari kasuwa a kauyen na Sundumina.
Kakakin ya kara da cewa, kudin babur din ya kai N400,000.
A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata laifin, an gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare da ke Birnin Kudu domin gurfanar da shi a gaban kuliya.