Hukumar shirya jarabawa ta yammacin Afirka (WAEC) ta sanar da wani shiri na bullo da tsarin gudanar da jarabawar kammala sakandire (WASSCE) ta kwamfuta (na’ura mai kwakwalwa).
Shugaban hukumar na Nijeriya, Mista Patrick Areghan ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Legas a ranar Asabar.
- Cutar Mashako Ta Kashe Yara 14 A Jihar Jigawa
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
Areghan, wanda ya yi tsokaci kan irin nasarorin da hukumar ta samu a karkashin kulawarsa, duk da cewa, shugaban ya fara shirin mika ragamar shugabancinsa a ranar 1 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa, bullo da tsarin gudanar da jarrabawar ta hanyar Kwamfuta (CBT) shi ne babban muradinsa a hukumar.
Areghan ya ce, baya ga bullo da shirin na CBT, yana kuma son ganin an daidaita dukkan ayyukan hukumar su zama na tsarin kwamfuta.