ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba

Ta Umurci Jami'an Tsaro Su Ɗauki Tsatstsauran Mataki

by Leadership Hausa
3 years ago
Gwamnatin Zamfara

A yau Asabar, Gwamnan Dauda Lawal, ya sanar da haramta haƙar ma’idanai ba bisa ƙa’ida ba, tare da umurtar jami’an tsaro su ɗauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka kama yana aikata hakan.

A tsawon shekaru, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin abubuwan da ke ta’azzara harkar ‘yan bindiga a faɗin Jihar Zamfara.

  • Masu Yi Wa Kasa Hidima 8 Da Aka Sace Sun Shafe Kwanaki 32 A Hannun Masu Garkuwa A Zamfara

Gwamna Lawal, a wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin ne domin daƙile wannan ɓarna ta haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da zimmar kiyaye rayukan al’umma.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa tuni gwamnatin ta bayar da umurni ga jami’an tsaro da su harbe duk wani wanda aka samu da aikata wannan ɓarna ta haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce: “Bayar da wannan umurni ya zama dole ne domin kiyaye rayukan al’umman Jihar Zamfara, domin kuma a yi wa ta’asar ‘yan bindiga garanbawul.

LABARAI MASU NASABA

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

“Haka nan kuma mataki ne da zai taimakawa gwamnatin jiha wurin tabbatar da kiyaye arzikinta, tare da rufe ƙofofin ɓarna da suke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na ɗaya daga cikin abubuwan da suke ta’azzara wutar ‘yan bindiga da rashin tsaro. Dole ne mu yi duk wani abu da za mu iya wurin ganin mun magance matsalar tsaro tare da wanzar da zaman lafiya a kowanne lungu da saƙo na Jihar Zamfara.” Inji shi.

Gwamnatin Zamfara
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    PalmPay Na Ƙara Wayar Da Kan Jama’a Game Da Hanyoyin Tuntuɓar Tallafi Na Hukuma Yayin Da Haɗarin Zamba Ke Ƙaruwa
  • Leadership Hausa
    ‘Yan Nijeriya Sun Gaji Da Uzurin Gwamnati Na Ƙarin Farashin Mai A Ƙasa
  • Leadership Hausa
    Bukatar Guje Wa Siyasantar Da Matsalar Tsaro
  • Leadership Hausa
    Gwarzuwar Ma’aikaciyar Gwamnati Ta Shekarar 2026 Mrs Zubaida Umar

MASU ALAKA

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi
Labarai

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna
Labarai

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola
Labarai

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Next Post
Tattalin arzikin sin

Tattalin Arzikin Sin Daga Janairu Zuwa Agusta Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata

LABARAI MASU NASABA

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

Wata Mata Ta Caka Wa Mijinta Wuƙa Kan Rigimar Wayar Salula A Bauchi

October 25, 2026
An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

An Yi Taron Karawa Juna Sani Na Murnar Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin A Birnin Fuzhou

October 25, 2026
Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

Nan Gaba Kaɗan Zan Bayyana Waɗanda Ke Daƙile Takarata – Pantami

October 25, 2026
Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.