Jami’an tsaro a daren Lahadi sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wa mazauna rukunin gidajen Tijjani Malumfashi da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.
‘Yan ta’addan sun yo tawaga mai yawa don kai farmaki yankin da wajen misalin karfe 11:00 na dare, inda suka rika harbe-harbe daga sassa daban-daban kafin su fara kutsa kai gida-gida don yin garkuwa da mutane.
- Wa Ya Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina?
- ’Yansanda Sun Ceto Mutum 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Wata majiya ta bayyana wa LEADERSHIP cewa, kafin isowar jami’an tsaro a wurin, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mazauna rukunin gidajen guda shida.
Majiyar ta yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa tare da dakile harin ta hanyar kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su bayan shafe kusan sa’a guda ana artabu da barayin mutanen.
“Babban Jami’an ‘Yan sanda na Malumfashi, tare da tawagar ‘yan sanda, sojoji, da ’yan banga ne suka yi nasarar dakile harin.
“An yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ‘yan ta’addar da jami’an tsaro kusan awa daya kafin su (’yan bindigan) suka yi taho-mu-gama, amma daya daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, wani fitaccen dan kasuwa, Alhaji Zaharaddeen, wanda aka fi sani da Danmaliki maharan sun sun harbe shi. Wadanda abun ya rutsa da su a halin yanzu suna samun kulawa a babban asibitin Kwandala da ke Malumfashi,” cewar majiyar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, ASP Aliyu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni ‘yan sandan suka fara gudanar da bincike kan harin.