Masu garkuwa da mutane sun sace kwamishinan yada labarai da yawon bude ido na jihar Benuwai, Matthew Abo.
Sun sace shi ne a daren ranar Lahadi a gidansa da ke a garin Abo Zaki-Biam da ke a cikin karamar hukumar Ukum.
- Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar NNPP A Jihar Benue Ya Fice Daga Jam’iyyar
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohowar Shugaban Kotun Gargajiya A Benue
A ranar 29 ga watan Agustan 2023 ne aka rantsar da shi a matsayin daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwar jihar.
Abo ya fito ne daga karamar hukumar Ukum wadda daya ce daga cikin yankunan kananan hukumomin jihar da ke fuskantar aikata manyan laifuka.
Wani ganau ya bayyana cewa, masu garkuwar da suka sace Abo, sun hawo Babura hudu zuwa gidansa da ke Zaki-Biam inda a nan suka yi awon-gaba da shi.
An rawaito cewa, masu garkuwar sun tilasta wa Abo hawa bayan daya daga cikin babur din masu garkuwar, inda kuma daya daga cikin masu garkuwar ya zauna a bayansa.
An ruwaito cewa, an kai rahoton afkuwar lamarin ga rundunar ‘yansandan jihar.
Sai dai, kakakin rundunar ‘Yansandan jihar, SP Catherine Anene, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan garkuwa da kwamshinan ba.
Amma sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Hyacinth Alia, Kula Tersoo, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, an sace shi ranar Lahadi da misalign karfe 8 na daren.
A cewarsa, tuni gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da sun ceto kwamishinan daga hannun masu garkuwar.