An samu barkewar yamutsi a asibitin kwararru na tarayya da ke jihar Gombe, biyo bayan zargin cire idon wata mata da ta rasu a asabitin.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, zargin ya auku ne ranar Talata wanda hakan ya hadasa fitowar wasu matasa da mata daga Unguwar Bagadaza, yankin da marigayiyar ta fito, inda suka gudanar da zanga-zanga.
- Da Dumi-dumi: Kotu Ta Kori Karar Da ADC Ke Yi Kan Gwamnan Gombe
- Kotu Ta Rushe Zaben Kakakin Majalisar Gombe Da Umarnin Sake Zabe Nan Da Kwanaki 30
Kazalika, an ruwaito cewa, ‘yansanda da sauran jami’an tsaro sun kawo dauki a gurin, inda suka garkame kofar shiga asibitin domin hana masu zanga-zangar kutsawa cikin asibitin.
Sai dai mahukuntan asibitin sun kyale wasu daga cikin ‘yan uwan marigayiyar sun shiga cikin asibitin da gawar don a yi gwaji.
Wata ‘yar mai rasuwar mai suna, Na’omi Ibrahim, a hirarta da LEADERSHIP ta ce, mahaifiyar ta mai suna, Halima Ibrahim, ta fara rashin lafiyar a ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka yi gaggawar kai ta asibitin don a duba lafiyarta.
Ta ce, bayan ta rasu an ajiye gawarta a dakin ajiye gawa na asibitin ind aka dauko a ranar Talata don a bizne ta.
A cewar Na’omi, bayan an bude gawarta don ‘yanu wanta su yi mata ganin karshe sai aka ga an cire idonta na hagu wanda hakan ya sa ta ankarar da ‘yan uwan.
Naomi ta ce, ana yi wa gawar wanka a asibitin an kuma saka gwar a cikin Akwatin gawa na asibitin.
Yanzu haka ana kan bincike don gano ainihin musabbabin faruwar lamarin.