Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya mikawa majalisar dokokin jihar karin kasafin kudi sama da naira biliyan 50 domin amince masa.
An gabatar da karin kasafin ne a yayin zaman majalisar wanda shugaban majalisar Hon. Isma’il Jibril Falgore ya karanta.
- NNPP Ta Kai Korafinta Ga Hukumar NJC Kan Kalaman Daya Da Cikin Alkalan Kotun Zaben Kano
- Martanin Da Ya Biyo Bayan Hukuncin Kotun Zaben Gwamnonin Kano, Bauchi Da Zamfara
Hon. Falgore ya sanar da majalisar cewa, bangaren zartarwa na neman amincewar majalisar kamar yadda sashe na 121(a) da (b) na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya tanada.
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta bayyana cewa, karin kasafin kudin na shekarar 2023 ya zama dole ne domin kara kaimi ga gwamnati tare da gaggauta aiwatar da ayyukan da ta saka a gaba don cimma manufofinta.