A kwanan baya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai rangadi a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, wanda ke kan gaba a kasar a fannin gudanar da aikin zamanantarwa. Inda shugaban ya jagoranci yadda za a gaggauta aikin zamanantar da lardin.
A yayin wannan rangadi, shugaba Xi ya ziyarci wurare 4 na garuruwa 2, inda ya shiga cikin wani karamin kauye, da wata cibiyar ciniki ta kasa da kasa, da wani dakin nuna fasahohin kula da batutuwan da suka shafi al’umma, gami da wani gandun al’adu mai kunshe da kayayyakin tarihi. Bisa tantance wuraren da ya ziyarta, da wasu bukatun da ya gabatar, za a iya fahimtar dabarar hanzarta zamanantar da al’umma mai salon musamman na kasar Sin.
Da farko, a dogara kan kirkiro sabbin fasahohin zamani wajen raya tattalin arziki, wannan dabara na daga cikin tunanin Xi Jinping ta fuskar tattalin arziki. Na biyu shi ne, dole ne a hada aikin zamanantarwa tare da manufar bude kofa ga kasashen ketare. Kana na uku shi ne, zamanantar da aikin gona da kauyuka wani muhimmin bangare ne na yunkurin zamanantar da kasar Sin. Sa’an nan na 4, zamanantar da dabarar gudanar da harkokin mulki da kula da al’umma, wani sabon bangare ne cikin tunanin shugaba Xi Jinping na gudanar da mulki. Daga karshe dai, ya kamata a lura da cewa, lardin Zhejiang wani wuri ne dake hade da al’adun zamanin baya da na wannan zamani da muke ciki kamar yadda ake bukata. Shugaba Xi Jinping, a nasa bangare, ya ba lardin Zhejiang wani sabon aiki mai muhimmanci, wato kokarin kirkiro sabuwar dabara don sauyawa da kuma raya nagartattun al’adun gargajiya, ta yadda za a iya raya al’adun kasar Sin na zamani yadda ake bukata. (Bello Wang)