Gwamnatin tarayya ta caccaki gwamnatin Jihar Zamfara bisa zargin da ake yi na sanya siyasa a sace daliban jami’ar tarayya ta Gusau (FUGUS) a jihar.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, shi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Litinin da ta gabata, ya nuna rashin jin dadinsa ga kalaman gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal, maimakon yaba wa jami’an tsaro da kuma hukumomin gwamnatin tarayya don gaggawar kokarin kubutar da daliban da aka sace, sai gwamnatin Zamfara ta saka siyasa cikin lamarin domin cimma birinta na siyasa.
- CMG Ta Kaddamar Da Wani Biki Don Fara Nuna Shirin “Journey Through Civilizations” A Kasar Peru
- NLC Da TUC Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki Mai Dogon Zango Ranar Talata 3 Ga Oktoba 2023
Ministan ya ce doka ta ba wa hukumomin gwamnatin tarayya ikon daukar mataki ba tare da wani dalili ba, domin tabbatar da tsaron rayukan ‘yan kasar da aka yi garkuwa da su, kamar yadda aka yi ga wadannan daliban.
Ya ce kasancewar hukumomin da ke da alhakkin ba su cikakken bayani kan irin wadannan ayyuka, hakan bai zama na sirri ba, kamar yadda gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana munin lamarin.
Ministan ya bayyana cewa domin kauce wa shakku, babu wani jami’in gwamnatin tarayya da ke tattaunawa da wani dan fashin daji ko kungiyar ‘yan bindiga.
Ya ce duk da haka gwamnati tana ci gaba da yunkurin gano duk wata hanyar da za ta iya haifar da tashin hankali tare da dawo da zaman lafiya a cikin al’ummomin da ‘yan fashi suka tarwatsa.
Ya ce idan al’ummomi suka yanke shawarar neman taimaka wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar nan domin su shiga tattaunawa, gwamnatin tarayya ba za ta yi gaggawar yin Allah wadai da irin wannan yunkuri na mutane ba.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin tarayya da hukumominta suna bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da duk wani nau’i na aikata mummunan laifuka.
Ya ce bambance-bambancen siyasa ko fada a tsakanin juna bai kamata a shigo da shi cikin wani muhimmin al’amari da ya shafi tsaron kasa ba, domin kauce wa ruguza kokarin sojojin ko kuma kawo cikas ga kokarin gwamnatin tarayya.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya a shirye take ta saurara tare da ci gaba da haad kai da duk masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan wajen samar da mafita mai dorewa ga matsalolin tsaro.
“Muna kira ga kowa da kowa da a hada hannu da mu domin samun mafita,” in ji minista.
Sai dai a bangare daya kuma, Gwamna Lawal, ya ce Gwamnatin Zamfara tana da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da hannu a shirya zaman sulhu da ‘yan bindiga.
A wata takardar da aka rabawa manema labarai, mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal tana da hujjoji masu tada hankali da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya kan sulhu da ‘yan bindiga.
Ya kara da cewa ministan labarai ya yi ri-ga mallam masallaci wurin yanke hukunci tare da yanke wa gwamnatin Zamfara hanzari.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun nemi karin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jami’anta suke jagoranta a Zamfara ba tare da sanin gwamnatin jiha ko shugabanni jami’an tsaron jihar ba.
“Muna da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da wannan zaman sulhu tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan bindiga a wurare mabambanta a Zamfara.
“Akwai ban takaici a ce ministan yada labarai zai fito bainar jama’a ya kore batun ba tare da ya nemi sani daga jami’an tsaro ko ‘yan uwanshi da ke da hannu dumu-dumu a lamarin ba. Mun tsammaci tun da kwararre ne a harka watsa labarai zai bi matakan da ilimi ya shardanta don tabbatarwa ko kore batun namu.
“Gwamnatin Jihar Zamfara tana matukar mutunta ka’ida tare da ganin kimar hukuma. Ba za mu fito kafafen watsa labarai muna fallasa sunayen jami’an Gwamnatin Tarayyan da ke wannan ta’asa ba, amma mun sanar da ‘yan Nijeriya don su nemi karin bayani daga Gwamnatin Tarayya.
“Muna so mu sanar da minista cewa jami’ansu na Gwamnatin Tarayya da ke jagorantar wannan zaman sulhu da ‘yan bindiga su ne ke siyasantar da matsalar tsaro ba Gwamnatin Zamfara ba.
“Ba mu san daga inda ministan ya samu kwarin gwiwan bugun kirji ya ce babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara ba, saboda ai mun bayyana wuraren da aka yi wadannan zama, irinsu Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.
“Muna sake nanatawa cewa sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara ba zai taba haifar da da mai ido ba. Sam! Ba wannan ba ne mafita ga matsalar, a yi amfani da karfi kawai a kauda su, wanna ita ce matsayarmu har gobe.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina biye wa ‘yan amshin Shata, ta yi bincike tare da wanke kanta daga aikin wadannan dillalan sulhu da ‘yan bindiga.”
Shi ma ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya musanta zargin cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da ‘yan bindiga a Jihar Zamfara a asirce ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.
Ministan ya bayyana haka ne a yayin da yake mayar da martani a wata takarda da ya aike wa Gwamna Dauda Lawal wanda ya yi zargin cewa, gwamnatin tarayya na tattaunawa da ‘yan ta’addan Zamfara domin ganin an sako mutanen da aka sace.
Ministan ya yi watsi da zargin, yana mai nuni da cewa “Gwamnatin Tarayya tana aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto ‘yan matan jami’an tarayya ta Gusau da sauran wadanda aka sace sun sake hadewa da iyalansu.
Ministan a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro (MOD), Attari Hope, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana kwarin gwiwar cewa, jami’an tsaro na hadin gwiwa da ke aiki ba dare ba rana za su ceto daliban.
Ministan ya ce, “Zargin karya ne kuma yaudara ce domin ma’aikatar tsaro ba ta umurci wani ko wata kungiya da su tattauna a madadin gwamnatin tarayya ba.”