Jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sanda da sojoji da Jami’an tsaro na farin kaya (DSS), sun kai samame a sansanin kungiyar IPOB inda take bai wa ‘ya’yan kungiyar horo a karamar hukumar Onicha Isu a jihar Ebonyi, Jami’an sun tarwatsa ‘ya’yan kungiyar bayan kashe ‘ya’yan kungiyar su Uku.
Kakakin Rundunar Chris Anyanwu ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a garin Abakaliki, inda ya bayyana cewa, Jami’an sun kai harin ne biyo bayan harin da aka kai wa motar sintiri ta ‘yan sanda a maraicen jiya wanda hakan ya janyo kisan wani dan sanda da ‘ya’yan kungiyar suka yi.
Fada Ya Barke Tsakanin Shugabannin ’Yan Bindiga, 2 Sun Mutu Yayin Rikicin A Zamfara
Ya sanar da cewa, Jami’an sun kuma gano bindiga kirar AK 49 daya da wata AK 47 daya da bindiga kirar AR da Albarusan bindiga kirar AR guda 147 da Albarusai na bindiga kirar AK-47 guda 38 da bindiga kirar gida guda daya.
Ya ce wasu daga cikin kayan da aka samu a wurin, sun hada da bindiga kirar gida guda daya da wata bindiga daya da kwabsar Albarusai da kuma wasu kayan tsafe -tsafe.