Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta kasar Argentina kuma zakarun kwallon kafa na duniya, sun kare matsayinsu na ci gaba da zama a mataki na daya a jerin kasashen da suka fi karfi a fagen kwallon kafa a duniya.
Cikin jerin kasashen da hukumar FIFA ta fitar ranar Alhamis, ya nuna cewa kasashe biyar na farko matsayinsu bai sauya ba duk da cewa an buga wasanni a cikin watan Satumba.
- A Shirye Sin Take Ta Inganta Hadin Gwiwa Da UNESCO Domin Samar Da Ci Gaba Da Zaman Lafiya A Duniya
- Manyan Batutuwa 7 Da Za Su Turnike Zauren Majalisa Bayan Dawowa Hutu
Argentina, wadda ta tsige Brazil daga matsayi na farko a jaddawalin a watan Afrilu, ta ci gaba da zama a kan gaba bayan ta doke Ecuador da Bolibia a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na shekara ta 2026.
Faransa ta biyu, wadda ta sha kashi a hannun Jamus a wasan sada zumunci a makon da ya gabata, ta rike matsayinta na biyu inda Brazil ke bin ta a baya, Ingila ce ta hudu sai Belgium a matsayi na biyar.
Kasar Portugal ce ta daya tilo a cikin kasashe 10 na farko da suka haura zuwa matsayi na takwas, yayin da Italiya ta sauko zuwa matsayi na tara bayan ta tashi 1-1 da North Macedonia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na 2024.
A kasashen Afrika kuwa Morocco ce kan gaba inda ta ke matsayi na 13 a duniya, sai Senegal ke biye da ita a matsayin ta biyu a Afrika amma ta 20 a duniya, Tunisia kuwa na matsayi uku a Afirka kuma ta 29 a duniya.
Tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Najeriya da kuma ta kasar Kamaru ba su sauya matsayi ba inda suke na shida da na bakwai a Afrika kuma matsayi na 40 da 41 a duniya.