A safiyar yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagororin JKS da na kasar, suka halarci wani biki a filin Tiananmen dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, don ajiye kwandunan furanni ga jaruman kasa da suka riga mu gidan gaskiya.
Tsoffin sojoji da iyalan shahidai da wakilai daga bangarori daban-daban, sun hallara a dandamalin tunawa da jaruman da suka yi shahada a filin na Tiananmen, don bikin ranar shahidan kasar karo na 10, wadda ta fado a ranar 30 ga watan Satumba, ranar dake zama jajiberen bikin kafuwar kasa.
- Kasar Sin Za Ta Kaddamar Da Binciken Duniyar Wata Mai Zuwa A Tsakanin Shekarar 2024
- Kasar Sin Na Maraba Da Baki Kwararru Domin Su Bada Gudunmuwa Ga Ci Gabanta
Da misalin karfe 10 na safe ne, dukkan wadanda suka halarci taron sun rera taken kasar, daga nan kuma suka jinjinawa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen ‘yantar da jama’ar kasar Sin, da ma gina jamhuriyar jama’ar kasar Sin, wadda aka kafa a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1949.
An ajiye manyan kwandunan furanni guda 9 a gaban dandamalin tunawa da jaruman. Xi da sauran shugabanni sun yi tattaki zuwa kusa da dandamalin tunawa da mazan jiya, inda ya mikar da kyallen da aka makala a jikin kwandunan kafin daga bisani ya jagoranci sauran manyan jami’an kasar don kewaya dandamalin tunawan, don nuna girmamawarsu.
A shekarar 2014, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, babbar majalissar kafa dokokin kasar Sin, ta amince da ranar 30 ga watan Satumba a matsayin ranar shahidai, domin tunawa da wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen neman ‘yancin kai da wadata a kasa, gami da kyautata jin dadin jama’a a zamanin yanzu.(Ibrahim)