Yaki da cutar Sikila (Amosanin Jini) uwar gidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriya Dauda, ta jagoranci Tattaki na farko kan yaki da cutar, daga ma’aikatar mata zuwa fadar mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello.
A jawabin matar gwamna Dauda, Hajiya Huriya da ta samu wakilcin kwamishiniyar ma’aikatar mata da kananan yara, Hajiya Nafisa Muhamda Maradun, ta bayyana cewa, sun shirya wannan tattaki ne tare da hadin guiwa da ofishin matar gwamna da ma’aikatar mata da kananan yara don fadakar da al’uma yadda ake yaki da cutar Sikila da yadda ta addabi alumma.
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Asirce: Sa-in-sa Ta Kaure Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Ta Zamfara
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Tir Da Yadda Gwamnatin Zamfara Ke Siyasantar da Matsalar Tsaro
Wakiliay ta uwargidan gwamnan ta bayyana cewa, yanzu haka a ma’aikatar mata akwai inda ake gwaje- gwaje dan gano cutar da kuma yin gwajin kyauta ba sai anbiya ba.
A wannan gangami akwai tallafi na kudi naira dubu goma ga masu dauke da cutar wanda mutane sitin za su amfana daga uwar gidan gwamnan jiha, Hajiya Huriya.
A nasa jawabin babban sakataren ma’aikatar mata da kananan yara, Dr. Habibu Yalwa, ya bayyana cewa, wannan gangami shi ne na farko da aka taba yi a wannan jihar ta Zamfara, don ganin an dakile yaduwar cutar Sikila a wannan jihar kuma yanzu haka an bude cibiya a ma’aikatar mata da fadar mai martaba Sarkin Katsinan Gusau don yin gwaje-gwajen don gano masu dauke da cutar da basu magani da shawarwarin kan yadda za a magance matsalar.
Mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, a jawabinsa, ya bayyana cewa, ya kamata wannan wayar da kai da fadarkarwa a yi shi a kafafen yada labarai don jama’a su fadaka sosai, kuma a hada da tallafin abinci don shi ne zai taimakawa masu dauke da cutar samun waraka saboda idan me ciwo na dauke da yunwa babu abun da za a iya ganowa.