Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya sanya dokar dakatar da hakar ma’adinai a kananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Ahmed Ibrahim Matane, ya fitar da yammacin ranar Litinin.
- Gwamnatin Zamfara Ta Fara Horas Da ‘Yan Sa-Kai Don Yakar ‘Yan Bindiga
- Muna Yin Siyasa Ce Bisa Tsammanin Gaba Za Ta Yi Kyau –Hajiya Halimah
Ta cikin sanarwar sakataren ya ce akwai bukatar a dakatar da hakar ma’adinai sakamakon yadda rashin tsaro ke kara kamari ‘yan kwanakin nan ta yadda ‘yan bindiga ke kai hare-hare.
Haka kuma ya kara da cewa an lura da cewa wuraren hakar ma’adinai na janyo masu aikata laifuka wadanda ke ci gaba da zama barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnatin jihar ta Neja, ta kuma yi gargadin cewa duk mutanen da aka kama suna hakar ma’adinai a yankunan da aka sanya dokar za su fuskanci hukunci.