Hukumar kula da gasar firimiya ta kasa ta ce kungiyoyi 20 da za su fafata a gasar ta bana za su sami naira miliyan 10 kowaccensu, bayan da ta sanar da ranar 30 ga watan da muke ciki na Satumba a matsayin ranar da za a fara gasar, biyo bayan dage ta har sau biyu.
Wannan na zuwa ne bayan da aka kara yawan kudaden da za a bai wa kungiyar da ta lashe gasar daga naira miliyan 100 zuwa naira miliyan 150 kuma aka kara yawan wanda za’a bawa wadanda suka buga gasar.
- Jawabin Shugaba Tinubu Kan Cikar Nijeriya Shekaru 63 Da Samun ‘Yancin Kai
- Uwargidan Gwamna Ta Jagoranci Tattaki Kan Yaki Da Cutar Sikila A Jihar Zamfara
Ta cikin wata takarda da hukumar ta aikewa kungiyoyin mai dauke da sa hannun shugaban gudanarwarta Dabidson Owumi, ta ce hukumar ta yi iya bakin kokarin ta wajen magance matsalolin da za su sa a sake dage fara gasar.
Sanarwar ta ce tana bukatar kungiyoyin cikin gaggawa su aike da lambobin asusun ajiyar bankinsu da za a sanya musu kudaden kafin lokacin da za a fara buga wasannin na bana.
NPFL ta ce nan gaba kadan za ta fitar da tsarin jadawalin yadda gasar za ta kasance da kuma yadda za a rinka haska ta kai tsaye a shafin hukumar da ragowar kamfanoni abokan hulda.