Wani dadadden salon magana na Sinawa na cewa “Hangzhou Aljannar duniya ce” saboda kyakkyawan yanayi, da dadadden tarihi, da al’adun da birnin ke da su.
A bana, bikin tsakiyar kaka na kasar Sin ya kasance jajebirin ranakun hutu na murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, kuma kasancewar ana tsaka da gudanar da gasar wasanni ta Asiya karo 19 a birnin Hangzhou, birnin ya zamo wani babban sansani na ‘yan yawon shakatawa.
- Adadin Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Kasashen Waje A Shekarar 2022 Na Kan Gaba A Duniya
- “Mafarkina Na Zuwa Sararin Samaniya”
Alkaluman da kamfanin hidimomin tafiye tafiye na Ctrip ya fitar sun nuna cewa, ya zuwa ranar 21 ga watan Satumban da ya shude, adadin masu yawon bude ido dake ziyartar Hangzhou, a wannan lokaci na gudanar gasar wasanni ta Asiya, ya karu da kaso 279 bisa dari.
Dandazon masu zuwa birnin Hangzhou yawon bude ido ya kai matsayi na 3 a kasar Sin, a wannan gaba da ake gudanar da hutun murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar ta Sin, adadin dake biye da na biranen Beijing da Shanghai, dake matsayi na daya da na biyu.(Saminu Alhassan)