Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa na ranar ‘yancin kai na kasa, ya bayyana karin Naira 25,000 ga albashin kananan ma’aikata har na tsawon watanni shida masu zuwa.
A cikin jawabinsa da aka yada a fadin kasar a safiyar Lahadi, Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yanke shawarar karin albashin ne ga kananan ma’aikata na wucin gadi kafin ta zartar da tsarin mafi karancin albashi domin rage radadin hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kafa Sashi Na Musamman A NPA Don Inganta Ayyukanta
- Jawabin Shugaba Tinubu Kan Cikar Nijeriya Shekaru 63 Da Samun ‘Yancin Kai
Tinubu ya kara da cewa, gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin ta kauda matsananciyar rayuwar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, inda ya ce an dauki matakai daban-daban daga kowane mataki na gwamnati don dakile kalubalen.
Shugaban ya ce, gwamnatin kuma ta fito da wasu tsare-tsare da za su amfani ‘yan Nijeriya kai tsaye da za su rage musu radadin hauhawar farashin kayayyakin masarufi.
Shugaban ya ce, dangane da harkokin sufuri, za a samar da manyan motocin bas mai amfani da gas mai rahusa da aminci a fadin Nijeriya.