Gwamnatin Tarayya ta yi taro da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC, a ranar 1 ga Oktoba, 2023, dangane da irin matakan da aka ɗauka domin shawo kan kiki-kakar da ta taso tsakanin su, tun bayan cire tallafin fetur.
Ɓangarorin biyu sun yi la’akari da waɗannan batutuwa:
i) Gwamnatin Tarayya ta yi sanarwar maida ƙarin albashin wucin-gadi na ma’aikatan gwamnatin tarayya zuwa naira 35,000, har tsawon watanni shida. An yi hakan ne bayan an sake tuntuɓar Shugaba Bola Tinubu.
ii) Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen gaggauta samar da motoci masu amfani da gas, ƙirar bas-bas, domin sauƙaƙa tsadar shiga motocin haya sanadiyyar cire tallafin fetur.
iii) Gwamnatin Tarayya za ta samar da jari ga masu ƙanana da matsakaitan masana’antu ko sana’o’i.
iv) Za a ɗauke biyan harajin VAT ga masu sayar da ‘dizal’ har tsawon watanni shida.
v) Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan naira 75,000 ga gidaje milyan 15. Amma za a tsittsinka kuɗaɗen gida uku, wato duk wata a riƙa biyan naira 25,000, har wata uku a jere.
Za a fara biyan kuɗaɗen daga Oktoba zuwa Disamba 2023.
Batutuwan Da Aka Tattauna A Wurin Taron:
i) Gwamantin ta roƙi ƙungiyoyin ƙwadago kada su tafi yajin aiki, domin dukkan abubuwan da ake so a cimma ba za su yiwu ba idan ma’aikata na yajin aiki.
ii) Ƙungiyoyin Ƙwadago sun bijiro da batun ƙarin albashi.
iii) An kafa ƙananan kwamitocin da za su bijiro da tsarin tallafin gwamnati, domin sauƙaƙa raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama, tun bayan cire tallafin fetur.
i) An nemi a sasanta rikicin da ke tsakanin ƙungiyoyin sufuri na RTEAN da NURTW na Jihar Legas da gaggawa.
v) NLC da TUC za su duba tayin yiwuwar fasa tafiya yajin aikin da Gwamnatin Tarayya ta roƙe su, domin a ci gaba da tuntuɓar juna.