Bankin Duniya ya ce ana sa ran bunkasar tattalin arzikin yankin kudu da hamadar sahara zai ragu a bana, sakamakon faduwar darajar kudi da ake samu a kasashen Afirka ta Kudu da Nijeriya da kuma Angola.
Bankin ya ce, ci gaban tattalin arzikin yankin zai ragu zuwa kaso 2.5 a cikin 2023 daga 3.6% da aka samu a bara.
- Takardun Karatun Tinubu Ba Na Bogi Ba Ne – Fadar Shugaban Kasa
- Kasar Sin Na Maraba Da Ziyarar Sanatocin Amurka
Bisa ga dukkan alamu, yankin bai samu wani ci gaba mai kyau ba tun daga shekarar 2015, saboda ayyukan tattalin arzikin kasashen yankin ya kasa tafiya daidai da karuwar al’umma da ake samu.
Babban masanin tattalin arziki a bankin Afirka, Andrew Dabalen, ya shaida wa AFP cewa, masu fama da talauci da marasa galihu a yankin na ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arziki sakamakon koma baya, sakamakon ci karuwar rashin ayyukan yi da ake samu.
Tattalin arzikin nahiyar da ya fi samun ci gaba, Afirka ta Kudu, wadda ke fuskantar matsalar makamashi mafi muni a tarihi, ana sa ran zai bunkasa da kashi 0.5% a bana.
Ana sa ran bunkasar tattalin arziki a manyan kasashen da ke hako mai wato irin su Nijeriya da Angola zai ragu zuwa kashi 2.9% ko kuma kashi 1.3.