Dan takarar shugaban kasa na jami’yyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, zai gudanar da taron manema labarai na duniya, a kan takardun kammala karantun Jami’ar Chicago na shugaban kasa Bola Tinubu.Â
Daya daga cikin hadimansa, Dele Momodu ne, ya bayyana hakan, cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X.
- NRC Ta Dakatar Ma’aikacinta Kan Karbar Kudin Fasinja Ba Bisa Ka’ida Ba
- Kwamishinan Benue Ya Kubuta Bayan Sace Shi Da Kwana 10
Sai dai, Dele bai sanar da takamaiman lokacin da Atiku zai yi wa manema labaran jawabin ba.
Idan za a iya tunawa, Atiku ta hanyar wata kotun da ke a kasar Amurka ya samu nasara a kan Jami’ar Chikago, ta fitar da takardar shaidar karatun Tinubu.
Kazalika, Atiku ya gabatar da bukatar hakan ne a gaban kotun gunduma da ke a Arewacin Illinois a Amurka, domin ta tilasta wa Jami’ar na ta fitar da takardar shaidar karatun Tinubu, bisa hujjarsa ta hakan, zai ba shi damar kalubalantar da yake yi na Tinubu a gaban kotu kan zaben shugaban kasa na ranar 25 na watan Fabrairun 2023.
Bugu da kari, Atiku ya bukaci samun takardun na Tinubu ne don ya kafa hujja a gaban kotun sauraron koken zaben shugaban kasa bisa jayyarsa ta cewa, Tinubu ya yi amfani da takardar bogi da ke dauke da shekarar 1979 daga Jami’ar Chicago, ya kuma gabatarwa da INEC, don ya tsaya takara a lokacin zaben 2023.