• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Karancin Kwan Gidan Gona A Jihar Neja

by Abubakar Abba
2 years ago
Gona

Ana ci gaba da fuskantar karancin kwan gidan gona a Jihar Neja, biyo bayan rufe gidajen gona da ake ci gaba da yi a fadin jihar.

Wannan dai ya afku ne, sakamakon tsadar kayan abincin kajin da masu sana’ar ke ci gaba da fuskanta.

  • Za Mu Tabbatar An Hukunta Masu Zaluntar Kananan Yara Da Mata – Kwamishina Rabi Salisu
  • Matsayin Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Japan Na Zuba Dagwalon Nukiliya A Cikin Teku Bai Sauya Ba

Rahotanni sun bayyana cewa, kwan kajin gidan gonar da ake turo wa zuwa jihar, musamman daga Jihar Oyo ya yi matukar raguwa, saboda tsadar da man fetur ya yi bayan cire tallafin man da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Haka zalika, an ruwaito cewa yanzu farashin kowane kiret guda da ake sayo wa daga gidan gona a jihar, ya doshi naira 2,200 sabanin yadda ake sayar da shi a baya kan naira 1,800.

Har ila yau, akwai kuma kalubalen rashin kyakkyawan yanayi da ke shafar yawan kwan da ya kamata a samu a gidan gona, wanda haka ke sa kajin na mutuwa.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

Wani mai sayen kwan, mai suna Isah Suleiman ya bayyana cewa, ya zagaya zuwa shaguna da dama don sayen kwan, amma bai samu ba.

Shi kuwa wani mai saye da sayar da kwan da ke Kasuwar Tunga a jihar, mai suna Christopher Ukaegbu ya bayyana cewa, kwan ya yi karanci a duk fadin jihar; kusan sama da mako biyu da suka wuce.

Shi ma wani manajan kajin gidan gonar da ke garin Minna a jihar ta Neja, Mista Adeyemo Adewale ya bayyana cewa, an samu karancin kwan da kuma tsadarsa a makon da ya gabata tare da tashin farashin abincinsu.

Bugu da kari, Mista Adeyemo ya ce, gidan gona da dama a jihar ta Neja da ake kiwon kajin gidan gonan; yawancinsu sun rufe, musamman saboda tsadar abincin da ake ciyar da kajin da kuma kwan da wasu manyan gidan gona da ke kawo wa Jihar Neja daga Jihar Oyo, sun dakatar sakamakon tsadar man fetur ya yi.

Adeyemo ya ci gaba da cewa, a kwanan baya wani gidan gona  da yake a garin Minna, da ake  kiwata kajin gidan gona wanda yawansu ya kai 3,000, tuni an rufe shi sakamakon wannan tsada ta abincin kaji, hatta mu ma da muka ci gaba da yin kiwon muna kokarin ne kawai, in ji shi.

A cewarsa, buhu daya na abincin kajin da muke saya a kan naira 8,500 a watan da ya wuce, yanzu kowane buhu ya tashi zuwa Naira 9,500.

Haka nan, masu gidan gonar da suka ci gaba da kiwata kajin, sun gaza samar da yawan kwan da ake bukata a kasuwanni, inda sauran mutane kuma ke ci gaba da nuna bukatarsu ta kwan.

Ya kara da cewa, a yanzu haka a gidan gonar tasa ba za a iya samar da bukatar kwan da mutane ke bukata ba na kaso 50 cikin 100 ba, inda ya ce, wasu masu zuwa gonar don sayen kwan, na far zuwa ne tun misalin karfe biyar na Asuba, domin sayen kwan da kuma kaji wadanda aka kyankyashe.

“Gidajen gona da dama da ake kiwon kaji a jihar, sun rufe sannan kuma kwan da ake kawo wa jihar daga kudancin kasar nan, ya ragu sakamakon tsadar da man fetur ya yi, sannan akasari, mun dogara ne a kan man dizel da muke zuba wa injin janareto,” in ji shi.

Saboda haka, a yanzu farashin man dizel ya karu daga naira 750 zuwa Naira 1, 050 kowace lita, wanda hakan ya kara jawo rufe gidajen gonar da ake kiwata wadannan kaji.

Shi ma wani manajan gidan gona da ake kiwata kaji na gidan gonar lSani Ahmadu, ya danganta karancin kwan kan wannan tsada ta man fetur da kuma tashin farashin abincinsu.

Kazalika ya kara da cewa, bukatar da ake da ita ta kwan a fadin jihar, ta fi karfin gidan gonar su iya samar da yawan kwan da ake bukata a jihar.

“Bukatar na da yawan gaske kuma ba mu da kwan da ake bukata a halin yanzu, ya kara da cewa, zuwan masu yi wa kasa hidima a sansaninsu da ke jihar, ya kara bukatar kwan a sansanin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
Noma Da Kiwo

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
Noma Da Kiwo

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
Next Post
An Horas Da Makiyaya Dabarun Shuka Ciyawar Shanu A Kaduna

An Horas Da Makiyaya Dabarun Shuka Ciyawar Shanu A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025
Gabar ‘Yan Bindiga A Tsakaninsu Ta Kara Tsanani A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako

October 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa

October 15, 2025
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara

October 15, 2025
Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima

October 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya

October 14, 2025
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani

October 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.