• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Tarayya Ta Dakatar Da Shirin N-Power

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Power

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin N-Power har illa-masha-Allah. 

Matakin na zuwa ne bisa wasu abubuwan da aka gano game da shirin wanda ba daidai ba.

  • Masu Laifi 222 Sun Mika Wuya, An Cafke 98 A Kano
  • Mutane Miliyan 826 Sun Yi Yawon Shakatawa A Yayin Ranaikun Hutu Na Kasar Sin

A cewar gwamnati, daukan matakin dakatarwar na zuwa ne bisa gano wasu kura-kurai da suke makale a shirin, kuma, tunin aka kaddamar da bincike kan yadda aka sarrafa kudaden da aka fitar tun lokacin fara aiwatar da shirin.

Ministar kula da harkokin jin-kai da yaki da fatara, Betta Edu, ita ce ta sanar da hakan yayin da take magana ta cikin wani shirin labaran talabijin din ‘TVC’ a ranar Asabar, ta yi ikirarin cewa wasu da suke cin gajiyar shirin ba su zuwa wuraren da aka turasu aiki, amma har yanzu su na tsamamanin a biyasu alawus-alawus na wata-wata.

Edu ta kara da cewa wasu da suke cikin shirin sun kammala cin moriya tun 2022 amma har yanzu suna cikin jerin wadanda ake biya.

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

“Dole ne mu waiwaya baya mu duba shirin N-Power kuma mun gano akwai kura-kurai don haka mun dakatar da shirin a yanzu har zuwa lokacin da za a kammala gudanar da cikakken bincike kan yadda aka sarrafa kudaden shirin N-Power.”

Ta ce, dole su gano mutum nawa ne suke cikin shirin a halin yanzu da kuma bashin da ke tattare da shi tare da gano mutum nawa ne bashin ya shafa, a cewarta gabaki daya suna son sauya fasalin tarin N-Power da ma fadada shi.

“Abubuwa da dama su na kan faruwa. Mun samu mutanen da ya dace su fita daga cikin shirin tun shekarar da ta gabata amma har yanzu suna kan ikirarin cewa suna koyarwa.

“Wasu lokutan idan muka tuntubi makarantu ko wuraren da aka turasu aiki sai a tarar ba su zuwa ba su nan gaba daya. Ba su aikin amma su na ta ikirarin cewa suna bin bashin alawus na wata tawas ko wata tara. Kusan kaso 80 cikin 100 ba su aikin amma suna ta neman a biyasu albashi,” ta shaida.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba
Manyan Labarai

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
Manyan Labarai

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Next Post
Makon Zinare

“Makon Zinare” Ya Kore Surutan Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasar Sin 

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.