Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fadawa shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan kasar Amurka Chuck Schumer, wanda ya jagoranci wata tawagar ‘yan majalisar dokokin Amurka don kawo ziyara kasar Sin cewa, a wannan duniya mai cike da sauye-sauye da rudani, yadda kasashen Sin da Amurka za su daidaita, shi ne zai tabbatar da makomar bil Adama.
Shugaba Xi ya shaidawa Schumer cewa, a matsayinsu na manyan kasashe biyu, ya kamata Sin da Amurka, su nuna himma, da hangen nesa, da kaiwa ga matsayin da kasashen duniya ke fata, da kokarin inganta jin dadin jama’arsu, da ingiza ci gaban bil Adama.
- Sin Ta Yi Kira Ga Falasdinu Da Isra’ila Da Su Gaggauta Kawo Karshen Tashin Hankalin Da Ake Yi Don Kare Fararen Hula
- An Kammala Aikin Tashar Samar Da Wutar Lantarki Da Kamfanonnin Sin Suka Zuba Jari A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo
Bugu da kari, shugaban na kasar Sin ya bayyana cewa, yayin da duniya da ma zamani ke sauyawa, har yanzu tunanin tarihi na zaman lafiya tsakanin kasashen Sin da Amurka bai sauya ba, haka kuma babban burin jama’arsu na yin mu’amala da yin hadin gwiwa bai canja ba, kana fatan da kasashen duniya ke yi na samun kwanciyar hankali da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka bai sauya ba.
Ya kuma bukaci bangarorin biyu da su mutunta juna, su zauna tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa domin samun nasara tare. Xi ya ce, manufar kasashen 2 ita ce, su daidaita da kuma kyautata alakarsu, da samar da hanyar da ta dace don yin cudanya da juna a sabon zamani na tarihi. Yana mai cewa, a wannan bangaren, ba za a taba iya maye gurbin mu’amalar fuska da fuska ba.” (Ibrahim)