Rundunar ‘yansandan jihar Borno, ta kama mutane 537 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da kisan kai, da tayar da hankali da sata, garkuwa da mutane, da cin zarafin mata, da sauransu, tare da yanke wa mutane 250 da ake zargi a watanni uku da suka gabata.Â
Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Mohammed Lawan, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum da ya sake duba kundin tsarin mulki na Borno, wanda ya ce ya kawo saukin hukunce-hukunce ga masu laifi.
Ya yaba wa mazauna Borno saboda kasancewa da tsaro da kuma ba da bayanai cikin gaggawa da amfani ga ‘yansanda don daukar matakin da ya dace.
Kwamishinan ya ce daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Hamisu Dauda, dan kauyen Panshani da ke karamar hukumar Shani na jihar, wanda ake zargin ya yi wa wata mata ‘yar shekara 62 fyade tare da yi mata fashin N42,700.
Ya ce akwai kuma shari’ar Umar Goni mai shekaru 25, wanda ya daba wa wani Zarami Modu, dan shekaru 35 wuka, bisa zarginsa da jan hankalin matarsa.
“Nasarar da aka samu ta samo asali ne sakamakon dokar da aka amince da ita a jihar Borno a kwanan nan ta 2023 da sauran abubuwan da suka shafe ta a wani bangare na kokarin Gwamnan Jihar Borno na mayar da zaman lafiya a jihar don samun ci gaba mai dorewa.”
Ya sake jaddada aniyar ci gaba da tabbatar da doka a jihar.