Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Talatar nan cewa, bayan shafe sama da shekaru 10 ana gudanar da bincike da samun ci gaba, sannu a hankali an samu bunkasuwar tsarin layukan dogo tsakanin Sin da kasashen Turai, wanda ya zama babban aikin da ake bukata da kuma alamar hadin gwiwar raya shawarar “ziri daya da hanya daya”.
Rahotanni na nuna cewa, alkaluman baya-bayan da aka fitar sun nuna cewa, adadin jiragen kasan dakon kaya tsakanin Sin da kasashen Turai a cikin shekaru 10 da suka gabata, ya kai dubu 78 dauke da kaya na manyan akwatunan TEU miliyan 7.4, wanda darajarsu ta kai sama da dalar Amurka biliyan 340.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin amfani da damar karbar bakuncin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, a matsayin wata dama ta zurfafa hadin gwiwa a aikace tare da dukkan bangarori, ta yadda layin dogo tsakanin Sin da kasashen Turai, zai ci gaba da hanzarta samun bunkasuwa da wadata, da bayar da gudummawa mai kyau ga tattalin arzikin duniya da ma amfanar da al’ummomin da hanyoyin jiragen kasan suka ratsa.(Ibrahim)