Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da wasu matasa ‘yan sa-kai kusan 1,500 da ta horar domin gudanar da aikin tsaro a jihar da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda.
Gwamnan Jihar Dikko Rada ne ya kaddamar da matasan wadanda jami’an tsaron soji da ‘yan sanda suka horar lokacin wani gagarumin bikin da ya samu halartar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin jihohi.
- Zulum Ya Daukaka Darajar Kwalejin Larabci Zuwa Babbar Cibiyar Yaki Da Akidun Boko Haram
- Dan Kwallon Nijeriya Na Cikin Hazikan ‘Yan Wasan Bundesliga Na Watan Satumba
Bayan horar da jami’an , gwamnatin Katsina ta kuma saya musu motoci da babura da makamai domin ganin ta taimaka musu wajen sauke nauyin da ya rataya a kan su na samar da tsaron da ake bukata.
Kwamishinan yada labaran jihar, Bala Zango, ya ce wadannan matasa da aka horar za su yi aiki tare ne da sojoji da ‘yansanda wajen ganin sun tallafa musu domin shawo kan matsalar da ta addabi jihar.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda wadanda suka hana zaman lafiya a wasu kananan hukumominta.
Tsohuwar gwamnatin Aminu Bello Masari da ta gabata, ta kai ga yin sulhu da wasu daga cikin ‘yan ta’addan wadanda suka sanar da ajiye makamansu, amma kuma daga bisani suka sake komawa daji.
Yayin gudanar da yakin neman zabensa, gwamna Dikko Rada ya sha alwashi kashe duk abin da jihar ta mallaka wajen ganin an shawo kan wannan matsala ta tsaro wadda ta hana zaman lafiya da kuma gudanar da harkokin ci gaba.