Sama da ‘yan bindiga 100 aka ruwaito cewa, an kashe a yayin da sojin rundunar sama ta Operation Hadarin Daji suka yi luguden wuta ta jirgin yaki a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.Â
An ruwaito cewa, luguden wutar wanda aka yi a ranar Talata, sojin sun yi shi ne a yayin da dandazon ‘yan bindigar suke shirin ficewa daga wani daji a jihar Zamfara zuwa jihar Kebbi, bisa nufin kai hare-hare a wasu kauyuka da ke a yankin.
- Kungiya Ta Yi Allah Wadai Da Wallafa Hoton Gwamna Uba Sani A Cece-ku-cen Rabon Mukaman Siyasa
- Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Taro Kan Rikicin Isra’ila da Falasdinu
Kazalika, wata babbar majiyar soji ta tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun samu bayanan cewa sojin na kan hanyar, wanda hakan ya tilsata su, dakatar da kudurinsu na zuwa kauyukan kai hare-haren, inda suka koma da baya zuwa hanyar Dansadau zuwa Maru.
Wannan ya bai wa sojin damar samun lago akan ‘yan binidar suka samu nasarar hallaka ‘yan bindigar sama da 100 ta hanyar luguden wuta ta sama tare da kone baburansu, inda kuma wasunsu, suka samu raunuka.
Bugu da kari, an ruwaito cewa, an birne gawarwakinsu a cikin kabari daya a dajin Sangeko na jihar Neja wasu kuma a Babban Doka a Maru a jihar Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar ta sojin sama ta Operation Hadarin Daji Kaftin Yahaya Ibrahim, ya tabbatar da yin luguden wutar, sai dai, ba a tabbatar da adadin ‘yan bindigar da suka mutu.
Bugu da kari, Daraktan yada labarai na rundunar sojin saman Nijeriya (DOPRI), Kwamando Edward Gabkwet, shi ma ya tabbatar da luguden wutar akan ‘yan bindigar a Zamfara, amma bai tabbatar da adadin ‘yan bindigar da aka kashe ba.
Zamfara dai, na daya daga cikin jihohi a arewacin kasar nan da ke ci gaba da fama da kalubalen hare-haren ‘yan bindiga, inda suma jihohin Nija, Kaduna, Sokoto, Kebbi da kuma Katsina, ke ci gaba da fuskantar wannan kalubalen.