Yau Alhamis ne aka gudanar da taron dandalin tattaunawa tsakanin kafofin yada labaru na bidiyo na kasa da kasa karo na 11, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya shirya. Shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cikin jawabinsa cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, ta hada kasa da kasa, kuma yanzu kasa da kasa sun amince da ita. CMG ya shiga aikin raya shawarar, da ganewa idonsa yadda ake raya ta, da kuma watsa shirye-shirye kan yadda ake raya shawarar. Don haka, yana son hada kai da takwarorinsa na duniya wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu, kyautata zumunci a tsakanin kasashen da ke raya shawarar, a kokarin ba da tasu gudummowar kan raya shawarar.
Jami’ai fiye da 140 daga kungiyoyin kafofin yada labaru na duniya da manyan kafofin yada labaru 108 daga kasashe da yankuna 63 ne suka halarci taron a zahiri da kuma ta kafar bidiyo. (Tasallah Yuan)