- Masana Sun Nemi A Samar Da Na’urorin Zamani Don Kare Makarantu
- Ana ci gaba da nuna damuwa kan hare-hare kan cibiyoyin ilimi da dalibai da ma’aikata a fadin kasar nan.
Binciken LEADERSHIP ya gano cewa kimanin yara ‘yan makaranta 1,591 aka sace a Nijeriya tun shekarar 2014 lokacin da ‘yan ta’adda suka sace dalibai 276 a garin Chibok na Jihar Borno.
Binciken ya kuma gano cewa sama da ‘yan bautar kasa (NYSC) 61 ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su tsakanin shekarar 2014 zuwa Oktoba 2023.
A yayin da akasarin wadanda aka yi garkuwa da su an sako su ba tare da an raunata su, wasu kuma har yanzu ana ci gaba da garkuwa da su kamar Leah Sharibu da aka yi sace a makarantar Dapchi a Jihar Yobe da daya daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist High School da ke Kaduna da daliban garin Damishi a karamar hukumar Chikun a Kaduna da wasu ‘yan bautar kasa takwas da aka yi garkuwa da su kwanan nan a kan babbar hanyar Zamfara da dai sauransu.
Hasali ma, wasu daga cikin ‘yan matan Chobok har yanzu ba a ceto su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su ba.
Masana harkokin tsaro da dalibai da sauran su, sun jaddada bukatar gaggawa kan kare makarantun daga masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ta hanyar aiwatar da shirin samar da tsaro a makarantu.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa bayan sace ‘yan matan Chibok da aka yi a Jihar Borno a shekarar 2014, gwamnatin tarayya a waccan lokaci ta kaddamar da shirin samar da tsaro a makarantu a wani mataki na tabbatar da tsare rayukan yara a makarantu domin su ci gaba da gudanar da karatunsu cikin kwanciyar hankali.
Wannan yunkurin hadin gwiwa ne a tsakanin gwamnatin Nijeriya da Majalisar Dinkin Duniya da masu fafutukar ilimi na duniya, domin samar da yanayi mai kyau ta yadda dalibai za su iya karantunsu ba tare da wani fargaba ba.
Dala miliyan 30 ne aka tara a lokacin kaddamar da shirin, wanda aka yi alkawarin kare makarantu da kuma ilmantar da matasa.
Duk da cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar tsare makarantu a shekarar 2019, amma an ci gaba da kai hare-hare a kan makarantu, musamman a yankin arewacin kasar nan, lamarin da ke haifar da koma baya kan harkokin ilimi ga yaran wannan yankin.
A watan Disambar 2022, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin ba da tallafin kudi ga shirin samar da tsaro a makarantu har na naira biliyan 144.8 da nufin kare makarantu daga hare-haren ta’addanci a fadin kasar nan.
Sai dai ministar kudi ta wancen lokacin, Zainab Ahmed ta bayyana cewa za a fara aiwatar da shirin ne tsakanin shekarar 2023 zuwa 2026.
Yayin da ake dakon aiwatar da shirin, masana harkokin tsaro da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki sun ce sanya na’urorin zamani a harabar makarantu zai taimaka wajen dakile sace yara ‘yan makaranta a fadin kasar.
Sun kuma yi kira da a bullo da wani darasi kan harkar tsaro a cikin manhajar karatu, don taimakawa wajen wayar da kan al’umma kan harkokin tsaro da wayar da kan dalibai da malamai.
A yayin da suke kira ga masu makarantu da shugabannin makarantu masu zaman kansu su samar da isassun matakan tsaro kamar shingaye, sun kuma jaddada bukatar yin amfani da kudaden da gwamnati ta ware na tsaro ta hanyar da ta dace.
LEADERSHIP ta yi nazari kan lokacin da aka yi garkuwa da daliban makarantu a fadin kasar nan, a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki suka yi ta kiraye-kirayen a samar da sabbin hanyoyin inganta tsaron makarantu.
Lokacin Garkuwan
A lokacin da ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka suka yi nisa wajen mayar da makarantu wuri na rashin tsaro, wanda ya yi sanadin sace yara ‘yan makaranta da ‘yan bautar kasa sama da 1,664 a Nijeriya tun daga shekarar 2014.
Watan Afrilun 14, 2014, an sace dalibai mata 276 a makarantar sakandaren ta Chibok a Jihar Borno.
A yayin da 57 daga cikin ‘yan matan makarantar suka tsere bayan faruwar lamarin, inda suka yi tsalle suka fita daga manyan motocin da aka yi jigilar su. Wasu kuma sojojin Nijeroiya ne suka samu nasarar kubutar da su a lokuta daban-daban.
An gano daya daga cikin ‘yan matan mai suna Amina Ali a watan Mayun 2016. Ranar 14 ga Afrilu, 2021, shekaru bakwai da sace ‘yan matan na farko, sama da ‘yan matan 100 suka bace.
A Ranar 19 ga Fabarairun An Yi Garkuwa Da Daliban Mata 110 A Makarantar Dapchi
Bayan shekaru hudu da kai farmaki a makarantar Chibok, ‘yan ta’adda sun kara kutsawa Jihar Yobe da ke yankin arewa maso yamma.
Ministan yada labarai da aladu na wancen lokaci, Lai Mohammed ya tabbatar da sace daliban 110 bayan da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a makarantar gwamnati na kimiyya da fasafa da ke Dapchi, a ranar Litinin 19 ga Fabarairun 2018.
Baya ga ‘yan mata biyar da suka mutu a lokacin faruwar lamarin, an ceto su tare da sada su da iyakansu a ranar 21 ga Maris, 2018 daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, sai dai daya daga ciki mai suna Leah Sharibu, wacce har yanzu tana hannun maharan.
An Yi Garkuwa Da Daliban Makarantar Kankara 303 A Ranar 11 Ga Disamba A Katsina.
A ranar Juma’a, 11 ga Disambar 2020, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makarantar sakandaren gwamnati ta kimiyya da ke Kankara a Jihar Katsina, inda aka yi garkuwa da dalibai maza har guda 303.
Sa dai kuma mako guda da sace daliban masu garkuwa suka sako su.
Bayan kwanaki biyu da sako daliban Kankara, a ranar 19 ga Disambar 2020, an yi garkuwa da daliban makarantar Islamiya guda 80 a Dandume duk dai a Jihar Katsina.
A wannan lokaci, an yi gaggawar ceto daliban bayan musayar wuta da jami’an tsaro, kamar yadda ‘yansanda suka ce.
Yunkurin garkuwa da daliban Dandume mai tazarar kilomita 64 daga Kankara, garin da aka yi garkuwa da dilibai maza tun farko.
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da 41 A Kagara Ranar 17 Ga Fabrairun A Neja
A ranar 17 ga Fabrairu, 2021, wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki makarantar kimiyya ta gwamnati da ke Kagara, karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja, inda suka yi garkuwa da dalibai, malamai, da sauran su a makarantar. Dalibai 27 ‘yan bindigan suka sace a wannan farmaki.
Ranar 26 Ga Fabrairun 2021 An Sace Dalibai Mata 317 A Jihar Zamfara
Kasa da kwanaki 10 da ‘yan bindigar suka kai farmaki garin Kagara, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai ‘yan mata 317 na makarantar sakandaren gwamnati da ke Jangebe a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 26 ga Fabrairun 2021.
Ranar 11 Ga Maris, 2021 Dalibai 39 Na Kwalejin Kula Dazuka Da Ke Afaka Aka Yi Garkuwa Da Su.
A ranar 11 ga Maris, 2021, an yi garkuwa da daliban kwalejin kula da dazuka har guda 39 da ke Afaka a Jihar Kaduna a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makonni kadan bayan wani hari makamancin haka a Jangebe na Jihar Zamfara.
Wadanda aka sace sun hada da mata 23 da maza 16. Jami’an tsaro sun samu nasarar ceto ma’aikata da dalibai 180 a washegari.
A ranar 5 ga Afrilu, 2021, gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa an sako mutane biyar daga cikin mutane 39 da aka sace a makarantar Afaka.
A ranar 8 ga Afrilu, 2021, jihar ta kara ba da sanarwar cewa an sake wasu dalibai biyar, yayin 29 ke hannun masu garkuwa.
A ranar 5 ga Mayu, 2021, gwamnatin jihar ta sanar da cewa an sako sauran dalibai 29 bayan sun shafe kwanaki 55 a hannun masu garkuwa.
Ranar 20 Ga Afrilun 2021 An Sace Daliban Jami’ar Greenfield 20.
A ranar 20 ga Afrilu, 2021, an yi garkuwa da akalla dalibai 20 da wasu ma’aikatan biyu na jami’ar Greenfield da ke kauyen Kasarami a karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna, yayin da wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su naira miliyan 800. A ranar 23 ga Afrilu, 2021, masu garkuwa da mutane sun kashe uku daga cikin daliban.
A ranar 29 ga Mayu, 2021, bayan kwanaki 40 a hannun masu garkuwan, an sake sauran dalibai 14 da suka rage. Iyayensu sun ce sun biya kudin fansa naira miliyan 150 da sabbin babura takwas ga barayin.
Ranar 30 Ga Mayun 2021 An Yi Garkuwa Da ‘Yan Makarantar Islamiyya A Neja
A ranar 30 ga Mayu, 2021, wasu gungun ‘yan bindiga dauke da makamai sun sace dalibai da dama daga wata makarantar Islamiyya a Jihar Neja.
Daya daga cikin jami’an makarantar ya bayyana cewa tun farko maharan sun dauki yara sama da 100, amma daga baya sun mayar da wasu wadanda ke tsakanin shekaru hudu zuwa 12.
Gwamnatin jihar ta ce maharan sun saki 11 daga cikin daliban wadanda kanana ne kuma ba su iya tafiya da nisa.
Ranar 17 Ga Yunin 2021 An Sace Dalibai 96 A Kwalejin Gwamnati Ta Birnin Yauri.
A ranar 17 ga watan Yuni, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Birnin Yauri a karamar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi, inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 96 da malamai 8 na kwalejin.
A Watan Yulin 2021 Dalibai 153 Na Makarantar Sakandare Ta Baptist Aka Sace
A watan Yulin 2021, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai153 na makarantar sakandare ta Bethel Baptist a garin Damishi da ke karamar hukumar Chikun a Kaduna.
A watan Satumba, 2023 An Sace Dalibai Sama Da 20 A Arewa Maso Yammacin Nijeriya.
Jami’an tsaro sun ceto dalibai 14 daga cikin 20 da aka sace daga wata jami’a a arewa maso yammacin Nijeriya tare da neman sauran wadanda aka kama, a cewar hukumomin makarantar.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a makarantar da ke gundumar Bungudu ta Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da dalibai, ita ce makaranta ta farko da aka fara sace dalibai tun lokacin da Shugaba Kasa Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayu.
Sama Da ‘Yan Bautar Kasa 61 Aka Yi Garkuwa Da Su.
A watan Oktoban 2018, an yi garkuwa da masu yi wa kasa hidima guda biyar.
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da masu yi wa kasa hidima guda biyar da ke tafiya zuwa sansanoninsu a jihohin Akwa Ibom da Ribas, da wasu fasinjoji biyu a watan Oktoban 2018.
Sai dai daga baya, kwamishinan ‘yansandan Imo, Dasuki Galadanchi ya tabbatar da cewa an kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane.
A Watan Fabrairun 2019, An Yi Garkuwa Da Masu Yi Wa Kasa Hidima 18 A Akwa Ibom.
A watan Fabrairun 2019 ne wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan bautar kasa har guda 18 a wurare daban-daban a Akwa Ibom. Daga baya an sako 14, kamar yadda kwamishinan hukumar zaben jihar, Mike Igini ya bayyana.
Haka kuma an yi garkuwa da wasu ‘yan bautar kasa hudu a yayin da suke dawowa daga Legas zuwa Fatakwal a Jihar Ribas a shekarar 2019. Rundunar ‘yansandan Jihar Ribas ta ce ta kubutar da su.
Wani dan bautar kasa, Abraham Amuta Abah da iyalansa ke zaune a Jentan Mangoro a garin Jos na Jihar Filato, wanda mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da shi a Jihar Borno a shekarar 2019.
A Watan Maris, 2020 An Yi Garkuwa Da Masu Yi Wa Kasa Hidima 4 A Zamfara
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu masu yi wa kasa hidima guda hudu da ke shirin zuwa Jihar Zamfara domin gudanar da aikin NYSC. Bayan kwana biyu ne aka ceto su.
Ranar 9 Ga Maris, 2020 An Yi Garkuwa Da ‘Yan Bautar Kasa 13 A Funtua.
Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta tabbatar da ceto ‘yan bautar kasa 13 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 9 ga watan Maris.
A Watan Oktoban 2021 An Yi Garkuwa Da Masu Yi Wa Kasa Hidima 2 A Zamfara.
An yi garkuwa da wasu masu yi wa kasa hidima guda biyu a kan hanyar Tsafe zuwa Gusau a Jihar Zamfara, bayan mako guda aka sako su.
Ranar 7 Ga Disambar 2022 An Yi Garkuwa Da ‘Yan Bautar Kasa A Abuja.
A ranar 7 ga watan Disamba, 2022, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Titin Arab da ke gundumar Kubwa a cikin Babban Birnin Tarayya (Abuja), inda suka yi garkuwa da dan bautar kasa mai suna Adenike da wasu bakwai tare da kashe wani mazaunin garin.
Ranar 22 Ga Agustan 2023 An Yi Garkuwa Da Masu Bautar Kasa 8 A Zamfara.
A ranar 22 ga watan Agusta, 2023, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu masu yi wa kasa hidima guda takwas a kan babbar hanyar Jihar Zamfara. Har zuwa yanzu ba a sako wasu daga cikinsu ba.
Wasu ‘yan bindiga a Jihar Ribas sun yi garkuwa da wasu ‘yan bautar kasa a yankin Rumuji da ke kan titin Gabas ta Yamma a karamar hukumar Emohua ta jihar. Sai dai biyar daga cikinsu sun tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.