Al’ummar unguwar Kabong da ke Gada Biyu a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato sun wayi gari da wani mummunar ibtila’in annoba da sanyin safiyar ranar Asabar biyo bayan bindiga da Taransifoma ta yi cikin dare da ta yi ajalin rayukan mutum 7 hadi da jikkata wasu da dama.
Wakilinmu ya labarto cewa wutar da ta tashi ta samu asali ne daga jikin na’urar rarraba wutar lantarki (taransifoma), inda mummunar gobara ta barke da ta janyo firgici da razani ga al’ummar unguwar.
- Jerin ‘Yan Nijeriya Da Suka Shiga Sahun Fitattun Musulmi 500 A Duniya
- Yadda Uwargida Za Ta Gyara Fuska Da Abubuwa Masu Sauki
A cewar ganau, wanda ya nemi kada a bayyana sunansa a jarida, ya ce, mutum bakwai ne suka mutu, kuma gidaje da shaguna da dama hade da kadarorin miliyoyin naira ne suka salwanta sakamakon tashin gobarar da ta samo asali daga fashewar taransifomar.
“Abun bakin ciki da takaici, biyu daga cikin mutanen da suka mutu din ‘yan gida daya ne, wanda hakan ya janyo bakin ciki da bacin rai ga ‘yan uwansu,” ya kara da cewa.
Kazalika, kamfanin rarraba wutar lantarki ta Jos (JED) ta tofa albarkacin bakinta kan annobar, inda ta ce ta kadu sosai bisa lamarin da ya faru tsakar daren ranar Asabar wanda ya shafi kwastominsu da ke amfani da na’urar rarraba wutar lantarki ta Kabong Primary a unguwar Kabong da ke kan hanyar Rububa a Jos, babban birnin jihar Filato.
A sanarwar da shugaban sashin yada labarai na kamfanin, Dr. Friday Adakole Elijah, ya ce, binciken farko-farko da aka yi ya nuna cewa babban layin wuta mai dauke da balbalin wuta shi ne ya shiga layin karamin layukan wuta inda hakan ya janyo wutar ta tsallake iyakar da aka ware mata.
Ya ce, dukkanin matakan da ya dace su bi wajen tabbatar da gano hakikanin abun da ya janyo tashin wutar za su yi, kuma sun dauki matakan gaggawa na kare faruwar hakan a nan gaba.
Daga bisani kamfanin JED ya mika ta’aziyyarsa da jajantawarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda dukiyarsu ya salwanta.