Wani hoton bidiyo da na gani ya nuna wasu kananan yara mata suna la’antar wasu sojojin Isra’ila da ke cikin shirin yaki a wani yanki na kasar Falasdinu da ke karkashin mamayar yahudawan Isra’ila, yayin da sojojin ke korar yaran su tafi gida. A gefe guda kuma ‘yan jarida ne ke daukar hotunan abubuwan da ke faruwa. Babu mamaki hakan ya sa sojojin kasa daukar wani mataki a kan yaran.
Amma abin da na lura da shi shi ne yadda yaran ke magana cikin fushi yana kara nuna yadda al’ummar Falasdinu ke cike da fushi da damuwa kan danniya da zaluncin da kasar Yahudawan Isra’ila ke ci gaba da nunawa a kasar su.
- Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Taro Kan Rikicin Isra’ila da Falasdinu
- Yadda Uwargida Za Ta Gyara Fuska Da Abubuwa Masu Sauki
A bayyane yake cewa, Falasdinawa sun kai makura kan irin abubuwan zalunci da suke fuskanta a wajen dakarun tsaron Isra’ila da munanan manufofin gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan kasashen Turai, musamman Amurka, Ingila, Jamus da Faransa. Wani rahoto da kungiyar ‘Save The Children’ ta fitar ya bayyana cewa fiye da rabin mutanen da ke rayuwa a wannan yanki na Zirin Gaza kananan yara ne da ba su san wani abu da ake kira zaman lafiya ko rayuwa cikin ‘yanci ba.
Marubuci Sun Tzu da ya rubuta shahararren littafin nan na dokokin yaki, wato The Art of War, ya bayyana cewa, ‘Idan ka killace makiyanka ka hana su sakat, ka hana musu duk wata dama ta ‘yanci to, idan fa tura ta kai su bango, za su fuskantoka da dukkan karfinsu, kuma ba za su ja baya ba!’ Za a iya cewa wannan shi ne kuskuren da kasar Isra’ila ta yi wajen killace yankin Zirin Gaza da kuntatawa Falasdinawa da take yi fiye da shekaru 17, cikin kuncin rashin wadatattun magunguna, rashin ingantaccen ruwan sha, da makamashi.
Babu shakka harin ranar Asabar da mayakan Hamas suka kai cikin Isra’ila ta kusurwoyi daban-daban ya girgiza gwamnatin kasar da jama’arta wadanda suka bayyana cewa tun kimanin shekaru 50 rabon da su ga irin wannan mummunan hari a kasar su, wanda a sanadiyyar haka an rasa rayukan Yahudawa da wasu baki ‘yan kasashen waje kimanin 1,200, ban da asarar dukiya mai yawa da harin ya haifar.
A wani bidiyo da dakarun Hamas suka fitar ta kafar yanar gizo game da yadda suka kai wannan mummunan harin ramuwar gayya, da ba a taɓa ganin irinsa ba, an jiyo mayakan na magana cikin harshen Larabci irin na mutanen Gaza, suna ambaton sunayen ‘yan uwansu da Isra’ila ta yi wa kisan gilla a yayin hare-haren da take kai wa, suna cewa; “wannan fansar ran dan’uwana wane ne!” ko “wannan fansar ran dana wane ne!” Suna ambaton wasu zafafan kalamai na bacin rai da kuncin zuciya, cikin takaicin abubuwan da Isra’ila ta dade tana aikata musu.
Koda yake biyo bayan wannan harin, dakarun kasar Isra’ila sun mayar da mummunan martani kan Birnin Gaza, inda suka barnata dukkan gine-ginen zirin mai girman kadada 365 da mutane miliyan 2 da dubu 300. A cikin kwanaki uku kacal Isra’ila da ke da karfin soja da manyan makaman yaki, ta kashe Falasdinawa 974, yayin da ta jikkata fiye da mutum 5,000. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu ta fitar ranar Laraba da safe, ta ce, dubban mutane suna cikin wani mawuyacin hali na jinya, da rashin magunguna da jini, da rashin wutar lantarki. Sun kuma kira al’ummar duniya su tallafawa mata da kananan yara da ke fuskantar barazanar kisa daga luguden wutar da sojojin Isra’ila ke ci gaba da yi musu. Bayan rasa dukkan abubuwan da suka mallaka, ciki har da muhallansu da wuraren kasuwanci da makarantu.
Wasu manazarta da suka tattauna da tashar talabijin ta Aljazeera sun koka da yadda hare-haren jiragen yaki da Isra’ila ke kaiwa cikin Gaza yana karewa kan gidajen zaman jama’a, da kasuwanni har ma da asibitoci, maimakon su fuskanci maɓoyar mayakan Hamas din, ko kuma su tunkare su gaba-da-gaba. Sai dai abin takaici mafi akasarin wadanda ke mutuwa mata ne da kananan yara.
Wata sanarwa da ta fito daga hukumomin kasar Isra’ila an jiyo suna umartar jama’ar yankin da su fita su bar garin, yayin da kasar ke shirin tura dakarun soji fiye da dubu 300 cikin yankin, don kai samame gida gida da nufin zakulo duk wani dan Hamas da ke garin, da nufin shafe su daga doron kasa baki daya. Duk kuwa da kasancewar Zirin na Gaza rufe yake daga sauran yankunan kasar Falasdinu, da duniya baki daya tsawon shekaru.
Ci gaba da kai hare-haren jiragen yaki kan raunanan al’ummar Gaza, hantara da lalata musu gine-gine gami da zubar da jinin mata da kananan yara, ya tayar da hankalin kowanne Musulmi har ma da wadanda ba Musulmi ba, saboda ganin halin kuntatawa, zalunci da kisan gillar da al’ummar Falasdinawa ke ci gaba da fuskanta.
Rahotanni daga kafafen watsa labarai na duniya, sun bayyana cewa, kungiyoyin al’umma daban-daban suna ta shirya zanga-zangar lumana da jerin gwano domin yin Allah wadai da ta’addacin gwamnatin Isra’ila a Zirin Gaza, ciki har da kungiyoyin Yahudawa masu sassaucin ra’ayi da ke nesanta kansu da addininsu da abin da suke cewa, siyasa ce da ke kara jawo musu bakin jini da kyama a duniya.
Mu da muke wannan sashi na duniya muna bibiyar abubuwan da ke faruwa cikin kunci da bacin rai na ganin halin da raunanan jama’ar Falasdinu ke ciki. Kodayake babu abin da za mu iya yi a kai da ya wuce mu jajenta musu kuma mu taya su da addu’ar ubangiji Allah Ya kawo musu dauki, kuma ya sakanta musu daga wannan zalunci da ake nuna musu. Wasun mu kuwa da ke mu’amala da shafukan sada zumunta na Soshiyal Midiya mun rika dora sakonni na yin tir da Allah wadai ga abubuwan da ke faruwa a wancan sashi na duniya.
Matsalar rikicin Isra’ila da Falasɗinu ba matsala ce ta addini kawai ba, akwai siyasar duniya, danniya da lalacewar shugabanci, wanda mu ma kan mu ‘yan Nijeriya kalubalen da muke fuskanta kenan. Sannan hakki ne na mutumtaka kowanne mai hankali ya nuna damuwa da mummunan zubar da jinin bayin Allah da kisan gillar da ke aukuwa da wasu bayin Allah raunana, da ke wani sashi na duniya, ba sai don zai amfanar da mu ta wata hanya ba. Duk da yake dai ni ba kwararre ba ne a wannan bangaren.
Za mu ci gaba da zuba ido, da nazarin abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, tare da addu’o’in samun zaman lafiya a kasar mu da duniya baki daya. Kuma ba za mu manta da gwagwarmayar mu ta cikin gida ta neman gwamnati ta kara tsaurara matakan tsaro domin dakile ayyukan ‘yan bindiga masu satar mutane suna garkuwa da su ba, da kuma kara kiran a kubutar da ‘yan matan Fugus, Dutsin-Ma, Sakkwato, da sauran sassan Najeriya da ake ci gaba da garkuwa da su, bayan sace su daga makaranta, inda suke neman ilimi.