• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Arsenal Ta Nuna Sha’awar Daukar Osimhen Idan Ya Yanke Shawarar Barin Napoli

by Rabilu Sanusi Bena
2 years ago
Arsenal

An bai wa Arsenal damar sayen dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen a kasuwar musayar ‘yan wasa, amma hakan zai sa ta rasa daya daga cikin manyan ‘yan wasanta Gabriel Jeauy.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da alakanta Gunners da karfafa zabin ‘yan wasan gabanta tare da Victor Osimhen a kasuwar musayar ‘yan wasa. Biyo bayan kashe fam miliyan 200 da suka yi a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta bazara, har yanzu akwai bukatar kungiyar da ke Arewacin Landan ta samu ‘yan wasan da suka kware wajen cin kwallaye.

  • Manchester United Zata Sayar Da Kashi 25 Na Kungiyar Akan Yuro Biliyan 1.3
  • An Bude Baje Kolin Canton Karo Na 134 A Guangzhou

Duk da cewa suna matsayi na biyu kuma har yanzu ba doke su ba a gasar Premier ta bana ba Arsenal na neman ganin ta tabuka abin azo a gani a wannan kakar. Gabriel Jesus da Eddie Nketiah su ne yan wasa masu zura kwallaye da Arsenal ta dogara da shi amma kuma har yanzu kwallaye uku kawai suka jefa su duka biyun abin da ya sa koci Arteta ke ganin akwai bukatar samun wanda zai jefa ma kungiyar kwallaye.

An alakanta Iban Toney na Brentford da kuma Ollie Watkins na Aston Billa duk da cewa ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya a Billa Park.

Sai kuma Osimhen, wanda ya kasance zabi mafi tsada amma wanda zai iya samuwa nan ba da jimawa ba.

LABARAI MASU NASABA

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

An ci gaba da yayata rade-radin cewa dan wasan na Nijeriya zai rattaba hannu a wani sabon kwantiragi a Napoli,sai dai al’amura sun yi tsami tsakaninsa da masu rike da kofin na Italiya a ‘yan makonnin da suka gabata.

Abin da ya sa wakilin Osimhen ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan kulob din saboda bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta game da tauraron.

Hakan dai ya kara tayar da hankali kan batun ficewarsa daga kungiyar kuma mai yiyuwa ne Arsenal ta dauko shi idan ya yanke shawarar barin Italiya. Hakan na iya faruwa a cikin watan Janairu domin Napoli ta fara neman wanda zai maye gurbin Osimhem kuma yana iya zama Gabriel Jesus na Arsenal wanda ka iya zama wani bangare na yarjejeniyar musaya.

Jesus na iya taka rawar gani a Napoli idan aka yi la’akari da muhimmancin dan wasan na Brazil tun da ya koma kungiyar daga Manchester City a bazarar da ta wuce.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid
Wasanni

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru
Wasanni

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Next Post
Manufar Kafa Kasashe Biyu Hanya Ce Daya Tilo Ta Warware Rikicin Palesdinu Da Isra’ila

Manufar Kafa Kasashe Biyu Hanya Ce Daya Tilo Ta Warware Rikicin Palesdinu Da Isra’ila

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025
Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai

Gwamnonin Arewa Sun Jajanta Wa Jihar Neja Kan Fashewar Tankar Mai

October 26, 2025
El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu

October 26, 2025
Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.