Gwamnatin jihar Kaduna ta bukaci al’ummar jihar da su rungumi dabi’ar tsaftace ruwa, yin amfani da shi ta yadda ya dace, yin amfani da abincin gida mai kyau nagartacce ba tare da yin barnarsu ba.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Mohammed Lawal Shehu ya fitar don tunawa da ranar Abinci ta Duniya ta 2023, mai taken “Ruwa shi ne rayuwa, Ruwa abinci ne, Bai bar kowa a baya ba.” Gwamna Uba Sani ya ce, akwai tsare-tsare masu yawa na inganta noma, kirkire-kirkire masu dorewa har ma da inganta kasuwar kayan abincin.
- Gwamna Uba Sani Ya Nada Dakta Mayere Sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna
- Ma’aikatan NIPOST Sun Ki Yarda Da Shugaban Da Tinubu Ya Nada, Sun Rufe Babban Ofishin
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamnatin Kaduna ta san muhimmiyar rawar da Ruwa ke takawa wajen tabbatar da samar da abinci, don haka, gwamnatinsa ta himmatu wajen samarwa al’umma musamman yankunan karkara ruwa mai tsafta kuma wadatacce.
“Gwamnatinmu ta himmatu wajen samarwa al’umma musamman yankunan karkara ruwan sha da abinci mai tsafta”
“Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Ruwa ta Jihar Kaduna (KADRUWASSA) tana aiwatar da shirye-shirye masu muhimmanci don inganta kiwon lafiya kamar hadin guiwa don fadada shirin samar da ruwan sha, tsaftar muhalli (PEWASH); samar da ruwa mai dorewa ga Birane da Karkara (SURWASH) don samar da ruwan sha; tsaftar muhalli da kiwon Lafiya (WASH)”
A cewar sanarwar, Gwamna Sani ya jinjinawa manoma kan jajircewarsu duk da kalubale da dama da suke fuskanta.