Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Huriyya Dauda Lawal, ta yi alkawarin tallafawa Mata Manoma da ke cikin Kananan hukumomi 14 na Jihar.
Hurriya Dauda, ta bayyana hakan ne a wajen bikin ranar abinci ta duniya da kungiyar mata manoma ta Kasa (NAWIA) reshen jihar Zamfara ta shirya a Gusau.
- Asalin Abin Da Ya Sa Aka Mayar Da Daukaka Karar Zaben Gwamnoni Zuwa Abuja Da Legas
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Samar Da Jami’an Tsaron Jihar
A ranar 16 ga watan Oktoba ne ake bikin ranar abinci ta duniya a kowace shekara, an ware ranar ne domin wayar da kan jama’a kan mahimmancin abinci mai gina jiki, da kuma bayyana kalubalen da miliyoyin mutane ke fuskanta a fadin duniya saboda rashin samun abinci mai kyau.
Da take jawabi a wurin bikin, Huriyya ta ce, “Miliyoyin mutane a duniya suna kokawa kan samun cin abinci ko da sau daya ne a rana, kuma dubbai suna mutuwa saboda yunwa.
“Duk da karuwar samar da abinci a duniya, har yanzu akwai mutane da dama da ke fama da yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
“Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin gwamna Dauda, na shirin bunkasa noma don farfado da tattalin arzikin jihar ta bangaren noma da ada muke tunkaho da shi”.
Hajiya Hurriya ta yi kira ga al’ummar jihar Zamfara musamman mata da su kara himma wajen yin noma, kuma ta bukaci jama’a da su kara yin addu’a domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
Daga bisani, Hajiya Huriya ta zagaya kasuwanni don ganin kayayyakin da Manoma mata ke nomawa kuma suke sarrafawa da kansu.
Anan take Uwar gidan gwamnan ta bawa manoman tallafin na naira miliyan uku na kananan hukumomin dan kara masu kwarin guiwa wajan sana’arsu.