A halin yanzu, ana gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan raya shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, kuma kafin shirya wannan muhimmin taro, wakiliyarmu ta zanta da wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya a birnin Abuja, ciki har da ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar, da kakakin majalisar wakilan kasar Abbas Tajudeen.
A zantawa da ministan wajen Najeriya Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, wannan taron yana da muhimmanci kwarai, kuma zai kawo sabon ci gaba ga Najeriya. A cewarsa gwamnatin Najeriya na mutunta dangantakarta da kasar Sin. A cikin ‘yan shekarun nan, kasashen biyu sun ci gaba da yin hadin gwiwa, tare da samun sakamako mai inganci. Najeriya ta yi imani cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” da Sin ta gabatar za ta inganta ci gaban kasashen Afirka, tana kuma fatan hada kai da Sin wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga bil’adama.
Tuggar ya kara da cewa, tun lokacin da kasashen Sin da Najeriya suka kulla dangantakar diplomassiya tsakaninsu, kasashen biyu suke gudanar da hadin gwiwa mai inganci a fannoni daban daban, tare da samun babban sakamako a fannonin amincewar siyasa da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya. Ya jaddada cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” tana da babbar ma’ana ga kyautata zaman rayuwar Najeriya da inganta ci gaban tattalin arzikin kasar, kana dandali na da kyau a fannin hadin gwiwar gina manyan kayayyakin more rayuwa da karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka.
Haka kuma, a nasa bangare, kakakin majalisar wakilan kasar Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa, kasashen Najeriya da Sin dukkansu kasashe ne masu tasowa dake da kamanceceniya, kuma suna tunkarar ayyukan raya kasa da dama. Yana mai cewa, shawarar ta kawo ci gaba masu amfani da yawa ga Najeriya, kuma an sami manyan nasarori a hadin gwiwar kasashen a fannoni daban daban.
Abbas ya ce, Sin ta kau da matsaloli da yawa a kan hanyar samun bunkasuwa a fannonin siyasa da tattalin arziki da al’adu da sauransu, musamman a fannin kau da matsanancin talauci, aikin da Sin ta yi ya kafa wata sabuwar hanya ga kasashe masu tasowa na duniya. Kuma a bisa tallafin Sin, an kyautata manyan gine-ginen more rayuwa na Najeriya, wanda ya kara kuzari ga ci gban tattalin arzikin Najeriya, don haka Najeriya tana godiya matuka da wannan karamci.
Ban da wannan kuma, game da maganganu kan wai batun “tarkon bashi” da wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma suke yi kuwa, Abbas ya ce wanann ba gaskiya ba ne, bangaren Sin ya baiwa Najeriya bashin da ake bukata a fannin hadin gwiwar gina manyan kayayyakin more rayuwa, kuma bashin da kasar Sin ta baiwa Najeriya mai karancin kudin ruwa ne da kuma tsawon lokacin biya. Ya kara da cewa, Najeriya za ta tsaya tsayin daka kan shiga cikin aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”, don samar da makoma mai kyau ga al’ummun kasar. (Amina Xu, Safiyah Ma)