Ministan Yada Labarai da Wayar da Kain Jama’a, Mohammed Idris, ya nuna damuwarsa ganin yadda akasarin ‘yan Nijeriya suka daina yin amanna ko gaskata kalaman shugabanninsu.
Ministan, ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), a Abuja.
- Majalisar Wakilai Za Ta Amince Da Kasafin Kudin 2024 Kafin Karshen Disamba
- Kotu Ta Daure Dillalin Tabar Wiwi Shekara 10 A Kano
“Abin da mu ke so shi ne a bar ‘yan Nijeriya su san gaskiya daga wadanda suka wajaba su bayyana masu gaskiyar. Ina ganin muhimmin abu ne sosai a ga cewa an dora tsarin isar da sako a kan turbar fada ko bayyana gaskiya, ta yadda wanda ake fada wa gaskiyar zai yi amanna da abin da mai fada masa gaskiyar ya ke fada.
“Wannan haka ne, saboda mun ga irin yadda amanna da gwamnati da kuma amincewa suka gushe ko suka zaizaye a zukatan jama’a, a kasar nan.
“Mun kai matakin da akasarin ‘yan Nijeriya ba su yi amanna da abin da shugabanninsu ke fada musu ba. Kuma su mutanen su ne suka zabi shugabannin da hannunsu.
“Saboda haka akwai bukatar mu fara ganin mun kankaro wa wannan gwamnati daraja, ta hanyar samun amincewa da amanna daga wurin ‘yan Nijeriya.
“Za mu yi wannan aikin haikan, bakin karfi da iyawar gwamnati, domin ganin jama’a sun dawo suna gaskata kalamai da bayanan gwamnati,” cewar Idris.
Ya kara da cewa fadin gaskiya shi ne matakin farko na nagartar mutum, domin idan jama’a suka san gwamnati na fadar gaskiya, to su ma fa masu bada rahotannin bayanai tsakanin tilas su rika fadar gaskiya.
Idris ya ce gwamnati na kokarin kara zaburar da jama’a cewa kowa ya kasance yana fadar gaskiya.
“Za mu fito mu yi kamfe na dakile masu yada labaran bogi da karairayi, wadanda hatsarin su zai iya kai wa ga ruguza al’umma ko kawo rabuwar kai.
“Kuma za mu ci gaba da kwadaitar da kafafen yada labarai su tsaya kan turbar bayyana gaskiya, wadda dama ita ce kyakkyawar dabi’ar da aka san kafafen yada labarai ke kan ta, kuma suke kan koyarwar ta,” cewar Minista Idris.
Dangane da labaran bogi, Idris ya ce wannan matsala ba ta Nijeriya kadai ba ce, abu ne wanda ya game duniya.
Ya ce idan aka hada hannu za a iya kawar da yaduwar su, ba tare da an take hakkin kowa ba.