Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ‘yan jarida a Nijeriya suna aiki a cikin mawuyacin yanayi, kuma sun cancanci samun ingantacciyar rayuwa, yadda za su samu damar gudanar da ayyukansu cikin sauki da walwala.
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris ne, ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), a Abuja.
- Kada Ku Bari ‘Yan Bindiga Su Shafe Baki Daya – Baraje
- Kotu Ta Daure Dillalin Tabar Wiwi Shekara 10 A Kano
Idris, ya ce wasu ‘yan jaridar ma sun rasa rayukansu wurin aikinsu.
A kan haka ya ce zai yi iyakar kokarinsa domin inganta rayuwar ‘yan jarida a gwamnatance.
“Za mu yi kokarin ganin ana bai wa ‘yan jarida dukkan hakkokin da suka cancanta a ba su.
“Saboda suna aiki a cikin mawuyacin yanayi, wani lokaci ma har rasa rayukansu suke yi, kamar yadda jami’an tsaro ke rasa nasu rayukan wajen tabbatar da tsaro.
“Sau da yawa za ku ga ‘yan jarida kafada da kafada a cikin jami’an tsaro idan sun fita yaki da ta’addanci. Da dama a cikin su kan koma gida da raunuka a jikinsu.
“Kuma kun dai ga yadda dan jarida ya rasa ransa a Zamfara saboda hare-haren ‘yan bindiga.
“To duk irin wadannan ba abubuwan jin dadin ba ne a ce a matsayina na Ministan Yada Labarai na faruwa. Ina so na ga karshen wannan matsalar.,” in ji Idris.
Sannan kuma ya kawo hanzarin dalilin da ya sa gwamnati ba za ta tsame ‘yan jarida ta yi masu karin albashi su kadai ba.
Ya ce akwai muhimmancin a duba ainihin yadda aikin nasu ke da tasiri da hatsari, domin a magance matsalolin da suke fuskanta.
“Ni a sahun gaba na ke na masu hankoron ganin rayuwar ‘yan jarida ta inganta. Kuma ina taka-tsantsan da sanin cewa suna aiki ne cikin da’irar iyakar gejin tattalin arziki kasarmu.
“Don haka ya zama tilas mu dubi wannan lamari baki daya, domin a karshe a yi mana kyakkyawar shaidar ‘yan kasa nagari.”