Fatima Bukar, ‘yar dan majalisar dokoki a jihar Borno, Bukar Abacha, mai wakiltar mazabar Ngala, wasu da ba a san ko su wanene ba a ranar Talata, sun kashe ta a yankin Dikechiri Bayan Gidan Dambe da ke a garin Maiduguri a cikin jihar Borno.
Mijin mariganyiyar ne ya dauki gawarta ya kai ofishin ‘yansanda da ke Gwange, inda ya ce, ya iske gawarta ne a gidansa, inda aka daure hannayen ta da kafuwanta, kana kuma ‘yar mariganyiyar mai shekaru biyu da haihuwa, tana kuka.
- ‘Yansanda A Kano Sun Musanta Zargin Daukar Masu Laifi Aiki
- Xi Ya Sanar Da Matakai 8 Na Tallafawa Raya Hadin Gwiwar Shawarar BRI Mai Inganci
Jami’an ‘yansandan, daga nan sai suka dauki gawawarta suka kai dakin adana gawarwaki na asibin koyarwa na jami’ar Maiduguri.
Lamarin ya jefa fargaba ga mazauna yankin, wanda hakan ya janyo mutane suka ta zuwa gurin da abin ya afku don ganewa idanuwansu. .
Bugu da kari, rundunar ‘yansanda ta jihar, ta cafko mijin mariganyiyar, Adam Alhaji Ibrahim.
Wata majiya kusa da dangin mariganyiyar ya ce, an kama Adam ne a daren ranar Talata bayan gwaman jihar, Babagana Umara Zulum ya umarci mahukunta su kai gawar Fatima zuwa asibitin kwararru don a gudanar da bincke akan gawarta.
Iyayanta da sun tsara za su yi mata jana’iza a ranar Laraba domin a bizne ta da misalin karfet 2 na rana a rukunin gidaje 707 da ke a Maidugur, kafin wannan umarnin na gwamna Zulum.