• English
  • Business News
Friday, August 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Kara Samun Karbuwa Tsakanin Rukunin Al’umma

by CGTN Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Kara Samun Karbuwa Tsakanin Rukunin Al’umma
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Baya ga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa da suka amince da shawarar “ziri daya da hanya daya”, a gabar da hankalin duniya ya koma ga taron kolin hadin gwiwar shawarar dake gudana a birnin Beijing na kasar Sin, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar nazarin watsa labaran kasa da kasa a sabon zamani ta tattara, karkashin jagorancin kafar talabijin ta CGTN, dake karkashin rukunin kafofin watsa labarai na kasar Sin CMG, da jami’ar Renmin ta kasar Sin, albarkacin cikar shawarar da kasar Sin ta gabatar shekaru goma cif da kafuwa, matasa dake tsakanin shekaru 18 zuwa 44, wadanda suka bayyana ra’ayinsu, sun amince da tunanin shawarar, da sakamakon da aka samu, tun bayan kafa shawarar shekaru goma da suka gabata zuwa yanzu.

Yayin kada kuri’ar jin ra’ayin jama’ar, an lura cewa, kaso 84.6 cikin 100 na matasan da suka bayyana ra’ayinsu, sun amince da “ruhin hanyar siliki” da kasar Sin ta gabatar, wato “hadin gwiwa cikin lumana, da bude kofa tare da yin hakuri, da koyi da juna, da cin moriyar juna domin samun ci gaba tare” . Bugu da kari, kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta nuna cewa, matasa masu karancin shekaru sun fi amincewa da shawarar, yayin da kaso 88.8 cikin 100 na matasa masu shekaru 18 zuwa 24, suka amince da “ruhin hanyar siliki”.

  • IMF Ta Yi Hasashen Tattalin Arzikin Kasar Sin Zai Karu Da Kaso 5 A Bana
  • Kasashe Masu Tasowa Da Abokai Sun Goyi Bayan Matsayin Kasar Sin Mai Adalci A Taron MDD

An gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ce ga matasa 3,857 dake kasashe 35, a kasashen Amurka, da Birtaniya, da Japan, da Afirka ta kudu, da Argentina, da Thailand, da Najeriya, da Peru, da Mexico da sauransu.  Baya ga rukunin matasa, shi ma shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya yi nuni da cewa, tun daga farkon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na farko a shekarar 2017 zuwa dandalin tattaunawar na biyu, sannan kuma ya zuwa yau, yanayin duniya ya canja. Musamman, yadda cutar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kowace kasa.

A yayin da duniya ke fama da sabbin matsaloli da manyan kalubaloli, yana fatan samun mafita ta hanyar shiga cikin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya”. Manufar shawarar “ziri daya da hanya daya” ita ce zamanintar da juna tare, da taimakawa wajen kara karfin kasashe na raya kansu. Daga raba kwarewar ci gaba zuwa horar da kwararru tare, daga bunkasa cinikayyar yanar gizo tsakanin kasa da kasa zuwa tattauna shirin ci gaba, Sin ta kawo sabbin damammaki ga duniya, tare da habaka hanyar zuwa zamanintarwa ta bil’adama. A jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar yayin bude taron hadin gwiwar shawawar karo na uku, ya bayyana cewa, ya dace mu hada kai wajen fuskantar kalubalolin dake gabanmu, ta yadda za a samar da wata makoma mai haske ga ’ya’yanmu da jikokinmu

Duk da cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta samo asali ne daga kasar Sin, amma shawarar ce ta duniya baki daya, kuma ta kawo alheri ga dukkanin bil’adama. (Ibrahim Yaya)

Labarai Masu Nasaba

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: IMFRashaSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Mutum 38 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe

Next Post

Tabbatar Da Daidaito Da Cin Moriyar Juna Suna Cikin Babban Ruhin Shawarar BRI

Related

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu
Daga Birnin Sin

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

2 hours ago
Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana
Daga Birnin Sin

Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

4 hours ago
Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing
Daga Birnin Sin

Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

4 hours ago
Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika
Daga Birnin Sin

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

6 hours ago
Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka
Daga Birnin Sin

Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

8 hours ago
Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
Daga Birnin Sin

Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira

9 hours ago
Next Post
Tabbatar Da Daidaito Da Cin Moriyar Juna Suna Cikin Babban Ruhin Shawarar BRI

Tabbatar Da Daidaito Da Cin Moriyar Juna Suna Cikin Babban Ruhin Shawarar BRI

LABARAI MASU NASABA

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

July 31, 2025
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

July 31, 2025
NIN-SIM: Masu Hulda Da Kamfanonin Sadarwa Sun Koka Kan Katse Layinsu Daga Tsarin Kira

Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC

July 31, 2025
Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

July 31, 2025
Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

July 31, 2025
Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

July 31, 2025
Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

July 31, 2025
Gwamnatin Borno Ta Nada Kwamitin Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi

Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu

July 31, 2025
Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

July 31, 2025
Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

July 31, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.