Babban Ministan Abuja, Nyesom Wike ya karyata rade-radin cewa, ya bada umurnin rushe wani bangare na Masallacin kasa da ke Abuja.
Wike ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gudanarwa na masallacin kasa na Abuja karkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar.
- Hukumar Kula Da Gidan Gyara Hali Ta Kori Jami’anta Biyu Tare Da Sanya Wa Wasu 35 Takunkumi
- Kasar Sin Za Ta Kammala Aikin Layin Dogo Daga Abuja Zuwa Kano Da Fatakwal Zuwa Maiduguri
Ya ce, “Ina so in fara daga abin da aka fada min; cewa na ba da umarnin rusa Masallacin kasa. Ina so ku sani cewa a siyasa, mutane za su yi amfani da abubuwa da yawa don yakar abokan hamayyarsu.
“Sarkin Musulmi na Sokoto, mutum ne da nake girmama shi, ba wai kawai ina ganinsa a matsayin babban yaya ba, kamar uba na dauke shi.
“Kasancewar sarkin shi ne Shugaban masallacin, duk wani abu da ya shafi Masallacin; Zan ba shi goyon baya a koyaushe.
“Obasanjo ne ya kaddamar da gidauniyar tallafa wa domin gyaran Masallacin. Babu wata gwamnati da ba za ta goyi bayan tabbatar da manyan abubuwan kasa ba. Muna da rawar da za mu taka wajen ganin an kula da wuraren ibada sosai.” inji wike
Wike ya bayyana cewa, masu amfani da addini don raba kan Jama’a, suna yi ne don cimma munanan muradan siyasarsu.
Tun da farko, Etsu Nupe ya bukaci ministan da ya tallafa wa aikin kula da masallacin, wanda ya ce an dade da daina tallafa wa.
Ya kuma roki ministan da ya kara baiwa kwamitin lokaci domin bunkasa filayen da FCTA ta ware wa masallacin.