Hukumar da ke kula da gidan gyara hali ta Nijeriya, NCoS ta kori wasu Jami’anta biyu tare da hukunta wasu 35 ta hanyar kakaba musu takunkumi bisa zarginsu da rashin da’a da kuma aikata wani abu da bai dace ba.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar, Umar Abubakar ya ce, dabi’ar jami’an na barazana ga tsaron Hukumar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, kakakin Hukumar ya bayyana cewa, korar na daga cikin kokarin tabbatar da da’a ga ma’aikatanta da kuma sanya kyawawan halaye na tabbatar da ingancin Hukumar.
Talla