Shugaban hukumar alhazai ta jihar Neja, Umar Makun Lapai ya hana shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Zikrullah Hassan hawa jirgi don Iulawa zuwa kasar Saudiyya.
An ga hakan ne a wani faifan Bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta, a yayin wata ‘yar hatsaniya da ta faru a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Lapai ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai daga Minna babban birnin jihar Neja. Kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.
Ya ce ba zai iya barin Shugaban Hukumar na kasa ya tafi aikin hajjin ba yayin da kashi hamsin cikin dari na maniyyatan jihar Neja da sauran jihohin ke ta watangaririya a filayen jiragen sama.
Lapai, ya kara da cewa bai kamata ba a matsayin Zikrullah Hassan na shugaban hukumar alhazai ta kasa, ya kama hanya ya tafi aikin Hajjin yayin da adadin maniyyata da dama da suka fito daga sassa daban-daban basu san makomarsu ba a bana.