Majalisar dattawa ta yi watsi da kudurin dokar kiraye-kirayen sake bude iyakokin Nijeriya da Nijar
Gwamnatin Nijeriya ta garkame iyakokin Nijeriya da Nijar tare da datse wutar lantarki tun a watan Agusta sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Nijar.
A cikin wani kudurin doka da ya gabatar yayin zaman majalisar na ranar Talata, Sanata Suleiman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya bayyana cewa rufe iyakokin ya tabarbare harkokin tattalin arziki a garuruwan kan iyaka kamar jihohin Sakwa-to, Zamfara, Katsina, Kebbi, Jigawa, Borno da Yobe.
- Kisan Sojojin Kasar Nijar 29 Ya Ja Hankalin Shugabannin Afirka
- Zulum Ya Bayar Da Umarni A Binciki Gawar ‘Yar Dan Majalisa Da Aka Kashe A Jihar Borno
Sanata Sumaila ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar sake bude iyakokin, ya lura cewa rufewar ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya da ke tabbatar da tsaro da jin dadin ‘yan kasa.
Sai dai kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisar dattawan ta kuduri aniyar mara baya ga kudurorin kungiyar raya tattal-in arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), kan halin da ake ciki a jamhuri-yar Nijar.
Sanata Akpabio ya bukaci Sanata Sumaila da ya janye kudirin, yana mai cewa sake bude iyakokin na da alaka da matsalar tsaro.
Nan take dan majalisar Kano ya janye kudurin.