Babban jami’in gudanarwa na kamfanin CWG Plc, Adewale Adeyipo, ya tabbatar da cewa bangaren fasahar Nijeriya shi ne ke kan gaba wajen samun jarin kasashen waje (FDI) a nahiyar Afrika, wanda ya kai kaso 40 cikin 100 na dukkanin jarin da aka zuba a shekarar 2022 da dala biliyan 1.5.
A fadinsa, sauran kasashen Afrika kamar Kenya ta samu dala biliyan 1, Afrika ta Kudu dala miliyan 800, Egypt kuma ta samu dala miliyan 700 gami da kasar Ghana mai samun dala miliyan 600.
- Kashim Shettima: Kasar Sin Ta Kasance Mai Kaunar Zaman Lafiya Da Bunkasar Arzikin Duniya
- Hajjin 2024: Wa’adin Adashin Gata Na Naira Miliyan 4.5 Ya Jefa Maniyyata Dimuwa
Ya shaida hakan ne a lokacin taron tsare-tsare na shekarar 2023 mai taken ‘Sabbin abubuwan fasaha domin gaba’ yana mai cewa akwai bukatar gwamnatin Nijeriya ta kasa azama wajen ribanta daga ban-garorin masu zaman kansu kuma a cewarsa gwamnatin na da gagarumar rawar da za ta taka wajen bunkasar kasuwancin fasaha a kasar.
Don haka, a cewarsa, bangaren fasaha zai zama tushen kirkire-kirkire a gaba, wanda zai yi tasiri wajen habakar tattalin arziki da kara wa Nijeriya tagomashi sosai.
Ya ce, “A bangaren tattalin arziki mai tasowa kamar a Nijeriya, akwai bukatar dole fa a samu wasu mu-tane da za a kirasu da matuka da za su jagoranci jan ragama gami da bullo da tsare-tsaren da za a hau kai a bi wajen daura lamura a mizani ciki har da yadda za a samu kudaden shiga da kuma ina aka nufa.
“Ina tsammanin CWG ta kasance cikin matukan nan idan ana maganar sauyi da sabbin abubuwa na kere-kere a bangaren fasaha a Nijeriya. Mu din kungiya ce da muka shafe shawon shekara 32 a wannan bangaren.”