Sakamakon zabukan da ya gabata da kuma kararrakin zabe da aka shigar a gaban kotu da ba a taba yin irinsa ba, ya kara sanya shakku ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan gudanar da sa-hihin zabe na gaskiya da adalci.
Kodayake dama, tun dawo da mulki ga gwamnatin farar hula a shekarar 1999, ake shiga kotu kan kararrakin zabe, amma a zaben bana, duba da adadin kararrakin zabe da ke gaban kotun daukaka kararrakin zabe, lamarin na da ban tsoro.
- Wani Matashi Ya Mayar Da Kusan Miliyan 100 Da Aka Turo Asusunsa Na Banki Bisa Kuskure
- Zaman Lafiya: MDD Ta Fara Yunkurin Samar Da Wani Sabon Tsari A Kaduna Da Katsina
A zaben bana, 2023, an gudanar da zabe a kujerun siyasa daban-daban har 1,280 tun daga kan kujerar shugaban kasa, ‘yan majalisar dattijai 109, majalisar wakilai ta tarayya 360, kujeru 782 na majalisar waki-lai a fadin jihohi 28 da kuma kujerun gwamnoni 28.
Cikin jimillar adadin, an shigar da kararraki 1,209 a gaban alkalai domin yanke hukunci, kamar yadda shugabar kotun daukaka kara (PCA), Mai shari’a Monica Dongban-mensem ta bayyana a lokacin bikin fara shekarar shari’a ta 2023/2024 a Abuja. Wannan ya nuna cewa, kashi 94.453 cikin 100 na kujerun da aka fafata, suna gaban alkalai.
Kujeru 71 ne kacal cikin 1,280 da aka fafata a zaben ba a garzaya kotu ba. Ya nuna kashi 5.547 cikin 100 kenan.
A watan Nuwamban da ya gabata, shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya koka kan yadda shari’o’i sama da 600 suke gaban hukumar gabanin zabe a kotuna da dama a fadin tarayyar Nijeriya, kamar yadda jaridar the guardian ta rahoto.
Mahmood ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga alkalai sama da 300 da za su gudanar da shari’o’i kan rikicin zabe.
Ya bayyana cewa shari’o’in da ke gaban hukumar zaben sun shafi yadda jam’iyyun siyasa ke gudanar da zaben fidda gwani, yanzun da aka kammala zabe, shari’o’in sun taso, yanzun INEC za ta yi shari’a kusan 1,209, tunda yawanci masu shigar da kara, sun shigar da INEC a cikin kokensu.