Xavi Simons na ci gaba da kasancewa daya daga cikin taurarin da ke tasowa a fagen kwallon kafar Turai bayan taka rawar gani tun bayan zuwansa RB Leipzig daga PSG a bana.
Dan wasan mai shekaru 20 yana haskawa a kakar wasa ta 2022-23 tare da RB Leipzig tun bayan zuwansa daga PSG a matsayin aro.
Simon watakila ya koma Paris Saint Germain bayan gana zaman aron da zai yi a Leipzig, amma kuma ya nuna cewar yana sha’awar samun buga mintuna masu yawa a duk inda zai koma.
- Tottenham Da Chelsea Na Zawarcin Ansu Fati Na Barcelona
- Za A Binciki Yadda Aka Karkatar Da Tallafin Korona Naira Biliyan 183.9
Abin da ake ganin da wuya ya samu a PSG, wanda hakan na iya zama sanadiyyar tashi daga kungiyar ga matashin dan wasan na kasar Holland.
Idan har Simon bai samu abin da yake bukata a PSG ba hakan ka iya sa ya tashi wanda kuma FC Barcelona za ta bi sahun sauran kungiyoyin Turai don duba halin da ake ciki da kuma ganin abin da ka iya faruwa na daga yiwuwar dawo da shi kungiyar da ya taba zama a lokacin kuruciya.
A cewar Diario SPORT, Barcelona na ci gaba da mai da hankali ga Simons, wanda tsohon dan wasan makarantar koyon kwallon kungiyar ne.
Duk da haka, kulob din na Spain zai fuskanci gasa daga manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai idan dan wasan tsakiya ya shiga kasuwar musayar ‘yan wasa.
Akwai kuma rahotanni dake cewa Real Madrid da Manchester City sun fito sun nuna maitarsu a fili dangane da matashin dan wasan inda suke bukatar dauko shi domin buga musu wasanni.