A wata sanarwa Gidainuyar TY Burutai Humanity Care Foundation’ ta bukaci al’ummar Nijeriya su kara hakuri tare da dukafa wajen gudanar da addu’o’i don samun nasarar mulkin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
Gidauniyar ta bayyana muhimmancin samar da ginshiki mai karfi a yayin da ake gida gida, kuma abin da Tinubu yake yi ke nan a halin yanzu a kokarinsa na samar da sabuwar Nijeriya.
- Buratai Ya Bukaci Kotu Ta Ci Tarar Sowore Naira Biliyan 10 Kan Bata Masa Suna
- Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai
Sanarwar ta samu sa hannun shugabanta, Alhaji Dahiru Danfulani, Sadaukin Garkuwan Keffi, ta kuma kara da cewa, fata da canjin da al’ummar Nijeriya ke bukara a rayuwarsu na nan tafe a don haka ya kamata a ci gaba da addu’a tare da hakuri a kan yadda abubuwa ke tafiya a halin yanzu.
“Wanda ta assasa gidauniyar, Ambasada Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai CFR, (Mai Ritaya) ya dade yana klira da cewa, ya kamata al’ummar Nijeriya su hada kai tare da aiki tare da don samar da Nijeriyar da kowa zai yi alfahari da ita, ba taer da bambancin siyasa ko kabilanci ba. Bayan an kammala harkokin zabe ya kamata dukkan ‘yan takara su dawo su hada hannu da shugaban da ya samu nasara don a tafi tare da a tsira tare. Wannan zai tabbatar da hadin kai da bunkasar kasa, abin da ake matukar bukata a halin yanzu”.
Gidauniyar ta kuma yi kira ga al’umma da su rungumi akidar tallafa wa mabukata, musamman a kan abubuwan da suka shafi kiwon lafiya, tallafin karatu ga matasanmu da kuma ciyar da matasa, wannan na da muhimmanci sosai saboda gwamnati ba za ta iya wadatar da dukkan kowa da kowa ba saboda haka dole mu zama masu tallafa wa juna a duk inda muka samu kanmu” in jii sanarwar.