Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa, sadaukar da kai da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi bai tsaya ga Nijeriya kaɗai ba, har ma da dukkanin nahiyar Afrika.
Ya ce: “Tun daga lokacin da ya kama aiki, an gan shi sosai a faɗin duniya ya na yayata manufofi da burukan Nijeriya da ma nahiyar Afrika.”
- NNPCL Ya Gargadi Masu Ɓoye Fetur Don Tsoron Ƙarin Farashin Man Da Samun Ƙarancinsa
- Wakilin Sin A MDD Ya Yi Kira Da A Aiwatar Da Matakan Gaggauta Dakatar Da Bude Wuta Tsakanin Falasdinu Da Isara’ila
Ministan ya faɗi haka ne a wurin wata walimar cin abincin dare wadda Ofishin Jakadancin ƙasar Angola ya shirya a Abuja a ranar Alhamis.
Ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya na da shauƙin ganin ya inganta mu’amalar da ke tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika, ciki har da Angola.
Idris ya ce, yanzu ana kallon Shugaban Ƙasa a matsayin uba a faɗin Afrika, wanda ke jagorantar ƙasar da ta fi kowace yawan jama’a da ƙarfin arziki a nahiyar.
A cewarsa, wannan ne ya sa aka naɗa Tinubu shugaban ƙungiyar ƙasashen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS, jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.
“A jawabinsa a wajen babban taron farko da ya halarta na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a watan jiya, ya yi magana mai gamsarwa ƙwarai kan dalilan da su ka sa Afrika ta ke buƙatar sauran ƙasashen duniya su yi ma ta adalci, abin da ya sa, ci gaban duniya ya na tattare ne da cigaban Afrika.
“Idan har duniya ta ɗauki batun samun ci gaba da gaske, tilas ne ta ɗauki batun ci gaban Afrika da gaske.” Inji Ministan.
Ministan ya ƙara da cewa mafarkin Shugaba Tinubu da burinsa shi ne ƙasashen Afrika su haɓaka dangantaka mai zurfi da ƙarfi a tsakaninsu wacce za ta ba da dama ga nahiyar ta samu matsayi mai girma da ƙarfi a fagen duniya da kuma samun dama mafi girma wajen samun ‘yanci mai ɗorewa da arziki. Duk abin da ya gaza kan wannan, to ba za mu yarda da shi ba.”
Ya yi la’akari da cewa idan har ba a haɗa kafaɗa aka yi mu’amala da haɗin kai tare ba, Afrika ba za ta cimma nasarar warware matsalolinta ba.