Kanar Garba Moyi ya yi murabus daga shugabancin kwamitin kirkiro da jami’an tsaro na Jihar Sakkwato kasa da mako daya da Gwamna Ahmed Aliyu ya nada shi mukamin.
Tsohon jami’in soji kana tsohon Kwamishinan Tsaro a Gwamnatin Tambuwal ya ajiye mukamin ne a kashin kan sa a bisa zargin da ake yi masa na cewar yana da hannu a sha’anin ta’addanci a Jihar kamar yadda ya bayyana a taron manema labarai a Sakkwato.
Jim kadan da Gwamnatin Sakkwato ta dora masa alhakin jagorantar kwamitin assasa rundunar tsaro ta jiha wadda za ta marawa kokarin hukumomin tsaro baya wajen yaki da ta’addanci a Jihar ne dimbin jama’a suka rika bayyana mabambantan ra’ayoyi kan cancanta da rashin cancntar tsohon sojan a aikin kwamitin samar da tsaro.
Fitattun Malamman Addinin Musulunci a Sakkwato, Sheikh Musa Ayuba Lukuwa da Murtala Assada duka a faifan bidiyo daban-daban sun bayyana karara cewar babban kuskure ne hannun ta kwamitin tsaro a hannun wanda aka jima ana zargin alakarsa da ‘yan ta’adda tare da sa hannu wajen hana al’umma bacci da idanu biyu, don haka suka bukaci Gwamnati ta canza shi.
A taron na manema labarai, Moyi ya bayyana cewar ajiye mukamin shine maslaha a gare shi domin kare kima da mutuncinsa ya fi gaban kowane irin mukami.
Ya ce yana da tarihin sadaukar da kai wajen bautawa kasa tare da ritaya a kashin kan sa bayan kwashe shekaru 35 a aikin soji a mukamin Kanar tare da shiga harkokin siyasa a in da ya fara da zama Shugaban Karamar Hukumar Isa. Ya ce jajircewarsa ga ci gaba da kyautata jin dadin jama’arsa ne dalilin da ya sa Gwamnatin Tambuwal ta nada shi Kwamishinan Tsaro, mukamin da a kashin kansa ya ajiye kafin karshen wa’adin mulkin tare da canza jam’iyya.
A cewarsa bisa ga sadaukarwarsa ne da sanin harkokin tsaro Gwamnatin Sakkwato ta nada shi mukamin shugabancin kwamitin. “A yau ina sanar da al’umma cewar na ajiye wannan mukamin a kashin kai na domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’umma.” Ya bayyana.