A cikin sanarwar da Hukumar Jiragen sama Ta GACA ta fitar a yau Laraba ta ce, an sake kara wani wa’adin jigilar maniyyatan aikin hajin bana zuwa kasa mai tsarki.
Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON), ta ce wannan damar wani sauki ne ga maniyyatan kasar nan su 3000 wadanda har yanzu ba a riga an kwashe su zuwa Saudiyya ba.
NAHCON ta ce, an samu wannan saukin ne bayan tattauna wa a tsakanin mahukuntan Saudiyya da na Nijeriya wacce Shugaban NAHCON Alh. Zikrullah Hassan, ya jagorabta a Saudiyya.
In za a iya tunawa, aikin na Hajjin bana na Nijeriya ya fuskanci kalubalen da suka shafi shirye -shiyen NAHCON da kuma a matakan sauran hukumiomin jin dadin Alhazai na jihohi.
A cikin sanarwar da NAHCON ta fitar ta ce, a wannan sabon tsarin, jiragen biyu Max Air da Azman airline za su ci gaba da yin jigilar maniyyatan daga Inda suka dakata, inda kuma NAHCON ta gama yin shiri da Flynas don a kwashe maniyyatan Kano da Abuja